Dalilin da ya sa matasan India ke mutuwa da kuruciya

Matan kabilar Dalit

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kabilar Dalits miliyan 230, na fuskantar tsangwama duk kuwa da ci gaban da aka samu a fannin siyasa da wayar da kan mutane a Indiya
    • Marubuci, Soutik Biswas
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, India correspondent

Kwararru a Indiya sun ce ana sa ran sabbin haihuwa su rayu tsawon shekaru 69, maimakon 72 kamar yadda ake hasashe a wasu sassan duniya.

Sai dai duk da hakan, shekarun da mutum zai iya rayuwa cikin rukunin mutane daban-daban a Indiya sun tsuke kamar yadda wasu bincike guda biyu suka yi bayani.

A kasar mai tarin al'umma, da yawan kabilu da addinai, mabiya addinin Musulunci suna cikin barazanar mutuwa da kankantar shekaru, idan aka kwatanta da mabiya addinin Hindu, kamar yadda masu binciken, Sangita Vyas da Payal Hathi da kuma Aashish Gupta suka bayyana.

Sun yi nazari akan bincike da kididdigar jami'an lafiya da na gwamnati, akan sama da mutane miliyan 20, a kuma jihohi tara na Indiya, wato kusan rabin al'ummar kasar biliyan daya da miliyan Hudu.

Masu binciken sun gano an samu raguwa matuka da shekaru hudu da kuwa na tsawon rai tsakanin kashi daban-daban na kasar. Binciken ya gano Musulmai za su yi tsawon rai da karin shekara guda idan aka kwatanta da mabiya addinin Hindu.

Bari mu rarraba wannan bayani ta hanyar amfani da jinsi.

Ana sa ran matan Indiya 'yan kabilar adivasis su yi tsawon rai da shekaru 62.8, sai kuma na kabilar Dalits za su yi tsawon rai da shekaru 63.3, sai kuma mata Musulmai da tsawon ran kashi 65.7.

Sai kuma matan Musulmi da ake sa ran za su yi tsahon rai da shekaru 66.5.

Yawancin Musulman Indiya, ba sa samun ayyuka masu gwabi-gwabi musamman fannin tattalin arziki

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mabiya addinin Musulunci 200 na sahun gaba a binciken

Sai kuma kason yadda tsawon ran maza a Indiya yake: mazan kabilar adivasis shekara 60, sai shekaru 61.3 ga Dalits, sai kuma maza Musulmai da shekaru 63.8.

Haka kuma ana sa ran namiji dan Hindu zai yi tsawon rai da shekaru 64.9.

Masana daga wata cibiya a Amurka sun ce yanayin da yawan shekarun ya danganta da inda ka fito. Misali tsawon rai tsakanin Amurkawa Bakake da Farare.

Tun da fatan da ake da shi kan tsawon rai a Indiya bai wuce kashi huɗu zuwa biyar ba idan aka kwatanta da Amurka, akwai tazara sosai a tsakaninsu.

Domin tabbatar da hakan, ta bunkasa fannin lafiya da tsaftar muhalli da lafiyar jama'a, Indiya ta samu gagarumin ci gaba ta wannan fannin, shekaru 50 da suka gabata, wasu 'yan kasar ba sa wuce shekaru 50 a duniya, amma a yanzu an samu karuwa da shekaru 20.

Sai dai labari maras dadin shi ne duk da an samu karuwar tsawon rai tsakanin mutane, akwai gagarumin gibi tsakanin arzikin 'yan kasar kamar yadda binciken Aashish Gupta da Nikkil Sudharsanan suna nuna.

A wasu lokuta, wannan gibin na taka rawa, misali; gagarumar ratar da ke tsakanin tsawon ran mazan kabilar Dalit da na Hindu na da bambanci.

An samu banbancin ne tsakanin shekarun 1990 zuwa tsakiyar 2010. Duk da Musulmai suna da tsaka-tsakin shekaru kuma an samu karuwa tsakanin hekarun 1997 zuwa 2000, an samu cike wannan gagarumin gibin shekaru 20 da suka gabata.

Mambobin kabilu daban-daban a jihar Maharashtra lokacin wata zanga-zanga da Satyshodhak Shetkari Sabha da Satyashodhak Gramin Kashtkari suka shirya kan rashin ruwa, da sare gandun daji a Azad Maidan 23 Oktoba, 2018 a birnin Mumbai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kabilu daban-daban har miliyan 120, suna daga cikin tarin 'yan kasar biliyan 1.4

Indiya na daga cikin kasashen duniya masu yawan al'umma, da addinai da kaliblu da al'adu daban-daban.

Akwai kabilar adivasis miliyan 120 a kasar, wadanda a duniya ake musu kallon tsiraru masu fama da talauci a tarihi a wasu yankunan kasar duk da siyasa da ayyukan ci gaban kasa. Sai kuma Dalits da suka kai miliyan 230 da har yanzu suke fuskantar tsangwama da nuna wariya.

Akwai Musulmai miliyan 200, wasu na uku cikin jerin masu yawan al'umma a Indiya, sun ci gaba da zama asahun gaba ta fuskar ci gaba, a wani fannin kuma sun fi kowa fiuskantar tashe-tashen hankula.

Me hakan ke nufi ta fuskar mabanbantan kungiyoyi ko kabilu?

Karanta bayanin kasa domin fahimtar yadda abin yake.

Masu bincike sun gano bambancin da ke tsakanin mutane, da arziki, da muhalli na kusan rabin al'ummar akwai tazara mai yawa.

Misali binciken ya gano kabilun adivasis da Dalits ba su da tsawon rai kamar mabiya addinin Hindu.

Domin gano sahihiyar amsa kan yadda nuna wariya da tsangwama ke taka rawa wajen yawan mace-mace, Indiya na bukatar ta kafa wata kungiya da za ta yi bincike kan hakan.

Akwai shaidu da suka tabbatar mana, dalilin da ya sa Musulmai suka fi adivasis da Dalits tsawon rai.

Ciki har da yadda aka bai wa yara tarbiyya tsuguno a bainar jama'a, matan Musulmai ba su cika kamuwa da cutar Kansa ko Daji na bakin mahaifa, da rashin shan barasa, da raguwar daukar rai da wasu ke yi.

Musulmai 'yan sa kai, na kungiyar Jamiat Ulama-i-Hind sanye da rigar kariya , tare da dan uwan wani da cutar korona ta yi ajali a mnakabarta lokacin bizne shi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ba a cika kammala rijistar mace-mace a Indiya ba

An kuma gano tsangwama da wariya da ake yi wa matasa musamman a makarantu, da yadda gwamnati ke tunkarar matsalar da tattaunawa da jami'an gwamnati sun kara taka rawa wajen sanyawa mutane tsananin damuwa.

An kuma alakanta hakan da karuwar tabarbarewar lamura. Sannan wadannan rukunin mutane ba sa samun ingantacciyar kula da lafiya da Ilimi da kuma rashin asibitoci masu kayan aiki.

Kungiyoyin al'umma kamar na duba gari, sun fi kowa fuskantar hadarin kamuwa da cutuka da mutuwa.

Masu binciken sun ce, sun gano yadda ake tunkarar batun lafiyar irin mutanen, suna kuma fuskantar kalubalen rashin maida hanhali da yin batun irin wadannad matsaloli da suka hada da na tattalin arziki da daidaito da suransu.

Ba sabon abu ba ne samun banbancin da ke tsakanin kungiyoyi a Indiya, akwai shaidu karara da ke nuna wagegen gibin da ke tsakani idan aka kwatanta da kasashe kamar Amirka, da Austra da Birtaniya.

Sai dai Indiya na bukatar karin bincike domin gano abin da ke haddasa mutuwa tsakanin matasan, da kuma binciken ko akwai nuna wariya da tsangwama da mutane ke fuskanta a cibiyoyin lafiya.

Rashin adana bayanai akan mace-mace miliyan 10 a kowacce shekara, bababr matsala ce. Domin an gano cikin mace-mace miliyan 10 an gano miliyan bakwai babu wani cikakken bayani da aka yi akan su, sannan miliyan uku ba ayi rijistar mutuwarsu ba.

Kamar yadda masu binciken suka bukata, sun ce ya zama dole a duba lamarin yadda ya dace musamman ''nuna wariya a fannin lafiya, da kuma inganta fannin lafiyar, su kuma zamo na amfanin kowa da kowa ba tare da la'akkari da addini ko al'ada ko kabilar inda mutanen suka fito ba.''

Presentational grey line