Madhya Pradesh: Abin da ya sa wata jiha a Indiya take rusa gidajen Musulmai

Asalin hoton, Madhya Pradesh police via Twitter
- Marubuci, Daga Zoya Mateen
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Delhi
Mutanen da suka rushe gidansa sun zo ne da sassafe, kamar yadda Sheik Mohammad Rafiq mai shekara 72 ya bayyana.
Mohammad Rafiq mai sayar da kayan sanyi a jihar Madhya Pradesh da ke Indiya da 'ya'yansa sun fuskanci wani dare mai tsawo. "Lokacin Azumin Ramadana ne, kasuwancinmu na farawa ne da yamma," in ji shi.
Lokacin da 'yan sanda suka isa bakin kofar shagonsu a safiyar Litinin, dukansu barci suke a lokacin. "Amma lokacin da muka ji wata kara mai karfi, sai muka gane cewa wani ya karya ginshikin kofar shagonsu," a cewarsa.
A waje, daruruwan jami'an tsaro ne a bayan katafila zagaye da gidansa, wanda yake a wata unguwar Musulmai da ke birnin Khargone, aka gaza samun wanda zai iya dakatar da su.
"Mun yi matukar tsorata ta yadda muka kasa cewa uffan, muka yi shiru muna zuba wa sarautar Allah ido."
An rushe shagunan Musulmai da dama a yankin Madhya Pradesh bayan wata hatsaniya da ta tashi a ranar 10 ga watan Afrilu, ranar bikin mabiya addinin Hindu da ake kira Ram Navami.
Wasu hotuna marasa kyan gani sun cika kafafen sada zumunta na wata katafila tana rushe musu gini, yayin da suka yi carko-carko suna kallo ba tare da samun taimako ba.
Wannan ya janyo fusata, mutane da dama na sukar cewa hakan wani kokari ne na danne Musulman Indiya, da yawansu ya kai miliyan 200, wanda Firaminista Narendra Modi ke yi da jam'iyyarsa ta BJP, wadda ke da karfin iko a yankin Madhya Pradesh.
Sai dai gwamnatin jihar ta dora alhakin wannan aiki kan Musulman,."Idan Musulmai za su kai irin wadannan hare-hare, to kada su yi tsammanin adalci," in ji Ministan Harkokin Cikin Gida Narottam Mishra.
An kuma nuna damuwa kan yadda "aka rika yin abubuwa da gayya" yayin rusau din, wanda masana suka ce babu hujjar yin hakan a shari'ance, kawai wani tozarci ne aka yi wa musulmai.
"Haka kurum kuna hukunta mutane ba tare da bin ka'ida ba, Ba kawai karya ka'ida hakan ya yi ba, zai iya haifar da wani tashin hankalin a nan gaba," in ji Ashhar Warsi, wani babban lauya da ke zaune a Indore.
"Sakon a nan shi ne: idan aka tambaye ka ko aka kalubalance mu ta wata hanya, sai mu zo mu ruguje gidanka da sana'ar da kake yi mu lalata ta."
An fara wannan rikici ne lokacin da wasu mabiya addinin Hindu masu yawa suka yi tattaki suka bi ta unguwar Musulmai da masallacin da suke ibada, suna ta kide-kide da neman rikici. A wasu yankunan Musulam rahotanni sun ce an rika jefe-jefe tsakanin masu tattakin da Musulmai mazauna unguwar.
Musulmai da dama sun zargi 'yan sanda da kyale 'yan Hindun suna kai musu hari. Hoton bidiyon wani mutum da takofi a zare ya nufi wani masallaci ya yi matukar girgiza kasar baki daya.
Shahbaz Khan mai shekara 28, ya yi zargin mabiya addinin Hindu sun karya wata hasumiyar masallaci a yankin Sendhwa da ke da nisan kilomita 137 daga Khargone - kuma suka kori Musulmai.
Amma bai ga tashin hankali ba sai washegari, lokacin da hukumomi suka zo kwatsam suka rushe gidansa, kamar yadda ya bayyana.
"Matata da 'yar uwarta suka dinga hawaye suna rokon a kyale mu mu kwashe kayanmu - akalla a kyale su su dauki Kur'aninsu daga cikin gidan - amma ko sauraronsu ba su yi ba," yana bayyana hakan ne daga cikin wani masallaci da yake fake.
"Babu abin da aka bar mu da shi.babu kuma wanda ya damu. Duk lokacin da muka je wajen 'yan sanda sai dai su kore mu."

Asalin hoton, Madhya Pradesh police via Twitter
Gwamnatin jihar ta bayyana karara cewa rusau din wani jan kunne ne ga wadanda ake zargi da jifan mabiya addinin Hindu. "Gidajen da jifan ya rika fitowa daga cikinsu sai sun zama kamar wasu duwatsu da za a rika jifa da su," in ji Mista Mishra.
Daga baya an fake da cewa gine-ginen, an yi su ne ba bisa ka'ida ba - 'yan sanda kuma sun yi ikirarin cewa suna kai harinsu ne kawai ga wadanda ke zaune a yankin ba bisa ka'ida ba.
Mai lura da yankin Khargone Anugraha P ya ce "an samu gaurayar duka mutane biyu ne a wajen".
"Zakulo masu laifi wani abu ne da zai dauki lokaci, don haka muna bincike a duka yankunan da aka yi wannan hatsaniya, muna rushe gine-ginen da aka yi ba bisa ka'ida ba," a cewarsa cikin bayanin da ya yi.
Sai dai Mista Rafiq ya ce babu wata hatsaniya da aka yi a yankin gidansa, "Ina da takarduna baki daya, komai na ka'ida ina da shi," in ji shi. "Yan sanda suka zo kawai suna rushe gida, suka ki saurare na."

Asalin hoton, Getty Images
Masana sun ce babu wata hujja da ta amince a rushe gidajen masu laifi ba tare da ba da wa'adi ba a dokar Indiya.
"Babu hujjar yin haka ko ta wane irin hali," in ji Warsi.
Hukumomi na daukar doka ne a hannunsu kuma kotu za ta duba hakan.
"Wannan ya nuna gwamnati dama na neman abin da za ta fake da shi ne ta yi wannan aiki."












