Zaben Faransa: Fafatawa tsakanin Le Pen da Macron masu bakin-jini a zaben kasar

- Marubuci, Katya Adler
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Europe editor
Yana da matukar wahala a samu fostar manyan 'yan takarar shugaban Faransa da ba a yaga ba.
Gabanin zaben shugaban kasa wanda zai samar da shugaban Faransa ranar Lahadi mai zuwa, ana ta rubuce-rubucen na zagi a ko ina: "mai mulkin kama-karya" ko "mai nuna wariyar launin fata " da "mai son fitattun mutane" da dai sauransu, a kan allunan talla na Marine Le Pen da Emmanuel Macron.
Baya daukar tsawon lokaci kafin ka gane ko da wa ake nufi a ko wane rubutu. Kiyayya mai zafin da masu kada kuri'a da dama ke nunawa ga daya ko kuma duka 'yan takarar biyu a wannan zabe ka iya ba ka mamaki.
Marine Le Pen ta saba ganin haka.
Wannan shi ne karo na uku da take tsayawa takarar shugaban kasa, kuma ta yi sanyi ba kamar yadda aka san ta a baya ba. Daga yanayin fankeken da take shafawa zuwa magana cikin tausasa murya da kuma mayar da hankali wajen ma'aikatan kasar Faransa da ke shan fadi-tashin rayuwa, a maimakon mayar da hankali wajen bayar da fiffiko ga abubuwan fitattun mutane: doka da oda da kuma harkokin shige da fice.
"Marine", kamar yadda a yanzu ta fi son a rika kiranta, ta yi ta matukar kokarin ganin cewa ta sauya kan ta zuwa mai ra'ayin sassauci da daidaito.
Na bullo mata da batun cewa masu sukar lamirinta na bayyana ta a matsayin "wacce ba ta cancanci a zabe ta ba"; suna mai bayyana ta a matsayin mai tsananin son fitattun mutane kana mai tsattsauran ra'ayi.
"Ni ba mai tsattsauran ra'ayi ba ce, yi hakuri!" ta mayar da martani. '' Gwamnati mai-ci ta samu jagoranci karkashin 'yan tsiraru da suka samu dama ta musamman, kuma ta 'yan tsiraru da suka samu babbar dama. Wannan shi ne gaskiyar lamari."
"Zan nemi takarar shugabancin kasar ne don na sauya haka. Zan kafa gwamnatin jama'a, ga jamaa'a…tare da sake mika mulki ga jama'a."
Idan za a yi adalci, ta ja hankulan da dama, da mafi rinjayen goyon ba ta taba samu ba a baya.
Nagette, wata matashiya Musulma da ke aikin ofis, ta shaida min cewa Le Pen tana iya "sauya dabi'unta a iya son ran ta" amma a zuciya ba za ta iya sauya ra'ayinta na mai tsattsauran ra'ayin siyasar fitattun mutane ba.
Za ta zabi Emmanuel Macron, in ji ta, don kayar da Le Pen a zaben.
Emmanuel Macron ya samu lokaci mai sauku a shekarar 2017. A yakin neman zabensa na shugabancin kasa na farko.
Lokacin shi farin shiga ne, wanda ke ikirarin cewa shi ba ya bin bangare, kawai yana mai alkawarin samar da makoma mai kyau ka duka 'yan kasar Faransa maza da mata.
Yanzu mulkinsa na shekara biyar ya zubar masa da kima, da suka hada da jagorantar yaki da annobar korona a duniya, da yaki a kasar Ukraine wanda ke yin barazana ga zaman lafiyar kasashen Turai, da cutar korona da kuma tashin hankalin kasar Russia da ake dangantawa da tabarbarewar tattalin arziki.
Madame Le Pen ba ita kadai ce ke fuskantar matsalar bata suna ba.
Masu sukar lamirin Macron na yi masa lakabi da "Jupiter" ko "shugaban kasan masu kudi''.
'Yan kasar Faransa na yawan magana a kan makala kyalle a kan hancinsu lokacin kada kuri'a a kashi na karshe na zaben shugaban kasar.
Game da zabar ''mafi inganci ko muni ne", za ka ji mutane na fada. Haramta wa dan takara mafi muni karbar ragamar shugabanci.
Ko da ana batun kayar da Marine Le Pen ko abokin karawarta ne, jam'iyun siyasar kasar Faransa za su dunkule wuri guda wajen hana masu tsattsauran ra'ayin kafa gwamnati.

Babban abin tambaya a nan shi ne ko masu kada kuri'a ga bangaren masu ra'ayin sassauci za su kaurace, saboda tsananin kin jinin Emmanuel Macron, ko da kuwa hakan zai bai wa Marine Le Pen damar shiga fadar gwamnatin Élysée ta bayan-fage.
Nuna rashin amincewa daga masu kada kuri'a da nuna rashin tausayawa daga masu kada kuri'a duka manyan kalubale ne ga Macron a ranar Lahadi fiye da ita kan ta Le Pen.
Ministan harkokin tattalin arziki na kasar Faransa Bruno Le Maire, ya shaida min cewa ya yi tsammanin kasashen duniya da dama, ba kasashen Turai kadai ba suna sane da abinda ke faruwa a wannan zaben: tunani biyu kan makomar kasar Faransa da tunani biyu kan makomar kasashen Turai, ya ce.
Musamman ma a daidai wannna lokaci da ake tsakiyar mummunan tashin hankali tsakanin Rasha da Ukraine.
Brussels da Washington na matukar kallon yadda za ta kaya a zaben, cike da nuna fatansu.
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky da fitaccen jagoran adawa na kasa Rasha Alexei Navalny duka sun yi kira da a sake zabar Macron.
Faransa ita ke da mafi yawan dakarun soji a Kungiyar Tarayyar Turai (EU). Ita ce ta biyu mafi karfin tattalin arziki a cikin kungiyar kana ita ce ta dauki babban matsayin kasashen Turai tun bayan ficewar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel daga harkokin siyasa, wanda ya sa Berlin ta yi sanyi a fagen harkokin kasashen duniya.
Macron na son bunkasa kungiyar EU, da kungiyar tsaro ta Nato da dangantakar kasashen gefen tekun Atlantika.

"Kana ganin idan idan ana yaki a kasashen Turai,'' Bruno Le Maire ya ce, "hakan abu ne mai kyau ga Faransa, ga kasashen kungiyar G7, ga duka kawayen kasar Faransa, su bari Faransa daya daga cikin muhimman kasashe masu karfi a Turai, ta janye daga cikin kawancen soji na NATO? '' ya tambaya.
Saboda wannan shi ne abin da Madame Le Pen ta dauri aniyar yi.
Mista Le Maire ya kuma yi gargadin cewa shirin Le Pen kan tattalin arziki zai kasance mai matukar muni, ya ce. Ba ga kasar Faransa kadai ba, amma ga daukacin kasashen Turai.
Kana zai yi nakasu ga abkoiyar huddar tattalin arziki ta kud-da-kud wato Birtaniya, ya bayyana.
Marine Le Pen ta yi tsananin kare manufofinta kan harkokin kudi, da suka hada da dakatar da biyan haraji ga masu shekaru kasa da 30 da kuma taimaka wa wadanda ke fama da matsalar tsadar rayuwar kasar Faransa.
Ta kuma yi ikirarin ba za ta sama mai barazana ga kungiyar Tarayyar Turai ba.
A wani bangare na yunkurinta na jan hankalin kara yawan masu kada mata kuri'a, Le Pen ta janye daga burin da ta ke da shin a cire Faransa daga cikin tsarin kudin bai-daya na euro kana daga "zaluncin Brussels".
Amma burinta da ta ayyana na rage yawan gudumawar Faransa ga kasafin kudin kungiyar ta EU, don rage 'yancin shige da ficen ma'aikata ba tare da amfani da fasfo din Schengen ba a fadin kan iyakokin kasashen Turai tare da ayyana karin dokar Faransa a kan dokar EU din, da kai tsaye ya sab awa yarjeniyoyin kungiyar ta EU, ka iya yi wa al'amuran EU din nakasu.
'Yar Majalisar Trayyar Turai Nathalie Loiseau, tsohuwar ministar Turai ta Macron, ta shaida min cewa ta shiga harkar siyasa don taimaka wa wajen hama masu tsattsauran ra'ayi kafa gwamnati.
Kada wanda ya ture batun yiwuwar samun galabar shugabancin kasar gefe guda, ta jaddada.
Ka tuna da ba-zatan samun galabar zaben Donald Trump da kuri'ar ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai wato Brexit, ta kara bayyanawa - lokacin da mutane suka kwanta barci, suna tunanin Birtaniya za ta cigaba da kasancewa cikin kungiyar ta EU, amma suka wayi gari da kasancewa cikin wani abu daban?
Har yanzu, idan da Marine Le Pen da kaucewa duk wani siradi ta zama shugabar kasa a wannan Lahadin, a cewar Nathalie Loiseau, zai yi wahala ta iya hada kawunan kasashe masu ra'ayi iri daya da ke son rarraba kungiyar.
Abokinta na kud-da-kud a kungiyar Turayyar Turai, Viktor Orban, na son kungiyar Tarayyar Turai ta cigaba da wanzuwa, ta bayyana, don haka kasarsa za ta cigaba da amfana daga hakan.
Taken yakin neman zaben Marine Le Pen da Emmanuel Macron dukan a ikirarin wakiltar duka mutanen kasar ta Faransa.
Idan aka yi la'akar da bambance-bambance tsakanin tsare-tsaren siyasa da halayyarsu, hakan ne abu ne mai kamar wuya.
Faransa kasa ce mai rarrabuwar kawuna.












