Marine Le Pen: Wace ce 'yar takarar shugaban Faransa da ke kyamar baki da hijabi?

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai fafata da shugabar masu ra'ayin riƙau Marine Le Pen a zagaye na biyu na zaɓen Faransa da za a gudanar a ranar 24 ga Afrilu.
Macron da Le Pen sun taɓa fafatawa a zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa a 2017.
Ƴan takarar biyu tuni suka ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe, inda Macron ya gode wa ƴan takarar da suka yi rashin nasara da suka yi kiran hana ƴan takarar masu ra'ayin riƙau yin nasara.
Le Pen kuma a nata ɓangaren ta buƙaci "dukkanin waɗanda ba su zaɓi Macron ba" su fito su mara mata baya, tana mai cewa a ƙuri'ar a zagaye na biyu tana da matukar muhimmanci ga al'umma da kuma ci gaba.
Wace ce Marine Le Pen?
Marine Le Pen an haife ta ne a 1968 a birnin Neuilly na Faransa, ƴar jagoran da ya samar da jam'iyyar masu ra'ayin riƙau ta National Front party, Jean-Marie Le Pen, da matarsa ta farko, Pierre.
Ta karatun shari'a a Paris tare da samun lasisin zama lauya.
Sau biyu ta yi aure kuma tana da ƴaƴa uku da mijinta na farko Frank Chafroy, (Giann, Louis da Mathilde). Bayan ta rabu da mijinta a 2000, ta auri Eric Laureau tsohon sakataren jam'iyyar National Front a 2022, kafin suka rabu a 2006.
Daga 2009 har zuwa 2019, Le Pen tana tare ne da Louis Elliott, wanda shi ne Sakatare Janar na jam'iyyarta daga 2005 zuwa 2010, daga baya mataimakin shugaban Jam'iyyar National Front.
Marine Le Pen ta bar aikin lauya a 1998 ta shiga siyasar mahaifinta, a cikin tawagar lauyoyin jam'iyyar.
Ta kasnce tare da jagoran National Front, Jean-Marie Le Pen, tun ƙuriciya da tafiye tafiyensa da kuma gangamin yaƙin neman zaɓe, a 1986 ta ayyana shiga Jam'iyyar a hukumance.

Asalin hoton, Getty Images
Farkon siyasarta
A 1998, Marine Le Pen ta lashe zaɓe a majalisar gundumar Norbadkale, a 2000 kuma ta zama mamba a jam'iyyar Politburo.
A shekarar ne ta jagoranci aikin inganta martabar jam'iyyarta a kafafen yaɗa labarai da kuma al'umma.
Batun "inganta martabar jam'iyyar ya fara samun karɓuwa ga mambobi da kuma magoya baya. Zaɓen yanki na 2002, Marine Le Pen ta samu ƙuri'u kashi 24.24 a birnin Lens a zagaye na farko, da kuma samun kashi 32.30 na ƙuri'u a zagaye na biyu.
Duk da ta yi rashin nasara, Marine Le Pen ta samu karɓuwa a zaɓen 2002, inda "tauraruwarta ta siyasa ta haskaka"
Tsarin Marine Le Pen a jam'iyyar National Front ta fara sauyawa da na mahaifinta tun 2003, lokacin da a karon farko ta yi magana kan "buƙatar ƙirƙirar tsarin Islama na Faransa."
A 2004 aka zaɓe ta a majalisar Turai, kuma ta kaɗa ƙuri'a kashi 42 na dokoki tare da sauran ƴan majalisar Faransa.
Ta fara samun saɓani da mahaifinta a siyasance a 2005 bayan wasu kalamansa cewa "mamayar da Jamus ta yi wa Faransa bai yi muni ba kamar yadda mutane suka yi tunani, duk da kura-kuran da wahala a iya kaucewa masu a babbar ƙasa kamar Faransa.
Tun lokacin, masana tarihi suka ce, ta kama hanyar gadar mahaifinta, ta hanyar yaɗa manufofinta a cikin jam'iyyar da kuma kafofin yaɗa labarai.

Asalin hoton, LEPEN
Saɓani da mahaifinta jagoran jam'iyya
Marine Le Pen ta nuna damuwa kan kalaman mahaifinta mai sarƙakiya, musamman waɗanda suka shafi yaƙin duniya na biyu, inda ta yi kiran a sake dokokin jam'iyyar da kuma yin watsi da matsayin mahaifinta.
Jean-Marie Le Pen na ganin ƴarsa ta yi masa maƙarƙashiya, ya shigar da ƙara amma kotu ta soke matakin sauya jam'iyyar da dokokin zaɓe.
Amma, jam'iyyar ta sanar da korar Jean-Marie Le Pen daga jam'iyyar a ranar 20 ga watan Agustan 2015, don ƴarsa ta zama shugaba.
Shugabancin jam'iyya
Bayan mahaifinta ya sanar da cewa zai sauka daga shugabancin jam'iyyar a 2010, kofa ta buɗe wa Marine na zama shugabar jam'iyyar National Front, abin da kuma ya faru a 2011.
Marine Le Pen ta tsaya takarar shugaban ƙasa a 2012, inda ta samu kaso 17.90 na ƙuri'u, sakamakon da ya kasance wani mataki mai muhimmanci ga jam'iyyar, inda sakamako mafi girma da mahaifinta ya samu shi ne kashi 16.86 a zaɓen shugaban ƙasa na 2002.

Asalin hoton, EPA
Marine Le Pen da jam'iyyarta sun ƙara samun ci zaba a zaɓukan Turai a 2014, inda ta samu ƙuri'u kashi 33.61% yayin da sauran jam'iyyun suka samu kashi 24.90.
A 2015, an samu ɓangarori na ra'ayin siyasa a majalisar Tarayyar turai ƙarƙashin inuwar "Al'ummar Turai da 'Yanci", kuma jam'iyyu da dama sun shiga ƙawancen da suka haɗa da Jam'iyyar Italian Northern League da Jam'iyyar Austrian Freedom, da Dutch Freedom Party da Jam'iyyar Vlaams Belang ta Belgium da kuma ƴar majalisar Birtaniya Janis Atkinson, da aka kora a jam'iyyar Ukip.
Le Pen ta sake fitowa takarar shugaban ƙasa a 2017, kuma ta fafata da Emmanuel Macron.
Bayan ta sha kaye a hannun Macron a zaɓen 2017, Le Pen ta sauya sunan jam'iyyarta ta National Front zuwa National Rally, ko da yake ba a sauya manufofin jam'iyyar ba.
Takarar shugaban ƙasa a 2022
A zagaye na farko na zaɓen, Macron ya lashe kusan kashi 28 na ƙuri'a, idan aka kwatanta da sama da kashi 23 da Le Pen ta lashe.
A hedikwatar jam'iyyarta magoya bayanta da dama sun ta yin murna, abin da ke nuna cewa sun gamsu da sakamakon ta yi rawar gani.
Wannan ne kaso mafi girma da Le Pen ta samu a zaɓuka uku na shugaban ƙasa da ta shiga.

Asalin hoton, Getty Images
Manufar Le Pen mai sarƙaƙiya
Babbar manufar Marine Le Pen da ta yi fice akai shi ne batun adawa da baƙi da kuma kiran a kori waɗanda suka shiga Faransa ba bisa ƙa'ida ba tare da ba ƴan ƙasashen waje waɗanda ba su da aiki wa'adin wata uku su samu aiki ko kuma su bar ƙasar.
Le Pen ta ce manufar mai muhimmanci ce ga ƙasa, kuma manufar na nufin za a fi ba waɗanda ke da shedar zama ƴan ƙasa fifiko kan buƙatar gidaje da sauran abubuwan more rayuwa.
Ana zargin Marine Le Pen a Faransa da nuna wariya da ƙyamar baƙi, amma ta musanta, tana cewa tana yaƙi ne da kwararar baƙi amma ba baƙin ba, tana mai cewa ta kare su a gaban kotu lokacin da tana lauya.
Ana ɗaukar jam'iyyar National Front mai tsananin ra'ayin riƙau, amma Le Pen ta yi watsi da wannan tana mai bayyana jam'iyyarta da "National Right".

Asalin hoton, Reuters
Le Pen da addinin Islama
Marine Le Pen, idan har ta ci zaɓe ta yi alƙawalin dakatar da aikin ginin masallatai a Faransa har sai an tantance inda suka samu tallafi, da tsawaita dokar zuwa ga hana saka tufafi da ke nuna addini a makarantu da wuraren taruwar jama'a, da haramta niqab da burqa da kuma mayafi.
Ta kuma yi kiran haramta yadda ake yanka dabbobi a tsarin shari'ar Musulunci, da sayar da naman halal a wuraren cin abinci ko kuma a tsari na addinin Yahudanci.
Kwana uku kafin zagaye na farko na zaɓen shugaban Faransa a 2022, ƴar takarar ta bayyana aniyarta ta saka haraji ko hukuntawa da haramta mata saka mayafi a lokacin wata hira da wata kafa a talabijin
A wasu kalamanta na baya bayan nan ta jajjada manufar yaƙi da abin da ta kira tsatsauran ra'ayin Islama" domin tabbatar da haka, idan har aka zaɓe ta za ta ci tarar matan da aka gani da hijabi a titi.
A watan Janairun 2021, Le Pen ta gabatar da shirinta na yakar "Akidun Musulunci" wadanda suka zama "na kama-karya" kuma sun zama "ko'ina" a idanunta, kuma wanda ta yi niyyar hanawa a kowane ɓangare na al'umma, inda za ta fara da saka mayafi.











