Emmanuel Macron: Musulmi sun yi zanga-zangar kyamar Faransa bayan Sallar Juma'a

Bayan kiran ƙauracewa kayayyakin Faransa, musulmi sun gudanar da zanga-zanga bayan Sallar Juma'a domin ci gaba da nuna fushi kan kalaman shugaban Faransa da kuma ɓatanci ga Annabi Muhammad.

Ana gudanar da zanga-zanga a kasashe da dama na musulmi don adawa da shugaban Faransa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana gudanar da zanga-zanga a kasashe da dama na musulmi don adawa da shugaban Faransa.
Fushin musulmi na ci gaba da ƙaruwa kan shugaban Faransa da kuma tunanin ɓatanci kan Musulunci da Annabi Muhammad, wanda ya haifar da kira a kauracewa kayayyakin Faransa da kuma yin gargaɗi ga Faransawa a ƙasashen Musulmi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fushin musulmi na ci gaba da ƙaruwa kan shugaban Faransa da kuma tunanin ɓatanci kan Musulunci da Annabi Muhammad, wanda ya haifar da kira a kauracewa kayayyakin Faransa da kuma yin gargaɗi ga Faransawa a ƙasashen Musulmi.
Zanga-zangar Allah wadai da kalaman Macron na Faransa a ranar Juma'a 30 ga watan Oktoba 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zanga-zangar ta samo asali ne tun zanen ɓatanci da mujallar Charlie Hebdo ta wallafa na ɓatanci ga Annabi Muhammad a jajibirin fara shari'ar mutum 14 da ake zargi sun kai mujallar harin ta'ddanci a 2015.
Zanga-zangar Allah wadai da kalaman Macron na Faransa a ranar Juma'a 30 ga watan Oktoba 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An yi zanga-zangar a Labanon inda magoya bayan Jam'iyyar Tahrir masu kishin Islama suka yi tattaki kan kyamar kalaman shugaban Faransa Emmanuel Macron game da musulmi
Turkiyya ce ƙasa ta farko da ta fara wannan zanga-zanga gabanin sauran wasu ƙasashen su dauka a duniya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jawabin da shugaba Macron ya yi bayan kisan wani malami Samuel Paty ya ƙara fusata al'ummar musulmi inda ya ce zai yaƙi abin da kira yaki addinin Islama da ya addabi duniya da rikici.
Zanga-zangar Allah wadai da kalaman Macron na Faransa a ranar Juma'a 30 ga watan Oktoba 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Malamin makaranta mai suna Samuel Paty wanda aka kashe ya nuna wa laɗibansa zanen da aka yi ɓatanci ga Annabi Muhammad
Kasar Jordan ta bi sahun kasashen duniya a wajen nuna ƙin jin Faransa da kalaman shugabanta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Faransa Macron ya ce kasar tana nan kan bakarta babu gudu babu ja da baya, ko yanzu kasar za ta ci gaba da yaƙi da masu tsattsauran ra'ayin addini
Zanga-zangar Allah wadai da kalaman Macron na Faransa a ranar Juma'a 30 ga watan Oktoba 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A babban birnin Libya Tripoli an yi zanga-zangar kyamar shugaban Faransa bayan Sallar Juma'a
An ta samun hare-hare ga mutanen Faransa a waje da cikin ƙasar kan wannan batu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan sanda a Moscow sun kama wani mutum da ke zanga-zanga a kofar ofishin jakadanci Faransa da ke Rasha, da zanga-zangar kyamar Faransa kan zanen batancin da mujallar Charlie Hebdo ta yi wa Musulmi
An kwashe kwanaki ana wannan zanga-zanagar a ƙasar Palasdinu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A yankin yamma da gaɓar tekun Jordan Falasdinawa sun ta ƙona hoton shugaban Faransa a wajen Jami'ar fasaha ta al-Aroub a birnin Hebron
Mata da yawa sun fito tare da ɗaukar matakan kariya na annobar korona yayin zanga-zangar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu zanga-zangar a Bagadada babban birnin Iraqi sun shafe kwanaki suna tattaki tare da kiran a fito babbar zanga-zangar da ta gudana a ranar Juma'a
Zanga-zangar Allah wadai da kalaman Macron na Faransa a ranar Juma'a 30 ga watan Oktoba 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Musulmi Masu zanga-zanga daga birnin Dhaka na Bangladesh
g

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsakiyar birnin Kabul na Afghanistan kenan a ranar Juma'a bayan idar da sallah, dubban mutane ne suka halarci zanga-zangar.