Zaben Faransa: Abubuwan da kuke bukatar sani kan yadda ake zaben Faransa

- Marubuci, Daga David Brown
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Faransa za ta tafi rumfunan zaɓe a watan Afrilu domin zaɓen shugaban ƙasa na zai jagoranci ƙasar tsawon shekara biyar.
Ga alama zaɓen zai kai zagaye na biyu.
Emmanuel Macron, shugaba mai ci, yana fatan samun nasarar wa'adi na biyu.
Ƴan takara
Ƴan takara 12 ne, takwas maza, huɗu mata.
Shida daga cikin manyan ƴan takara, uku daga ɓangaren masu ra'ayin riƙau a siyasar Faransa, biyu kuma daga ɓangaren masu rajin sauyi.

Emmanuel Macron ana kallon yana tsakiya. Yana wakilatar jam'iyyar Move kuma yana jan hankalin masu kaɗa ƙuri'a daga ɓangaren masu ra'ayin riƙau da masu neman sauyi.
Marine Le Pen da Eric Zemmour dukkaninsu suna ɓangaren masu ra'ayin riƙau inda ake ganin Mr Zemmour a matsayin wanda ya fi tsauri.
Valérie Pécresse ana ganin ta fi sassauci da ta fito daga ɓangaren Republicans.
Jean-Luc Mélenchon yana ɓangaren masu neman sauyi, kuma Yannick Jadot yana ɓangaren Greens.
Bayan samun koma baya, Masu ra'ayin kawo sauyi sun ja baya daga takarar.
Goyon baya ga jam'iyyar Socialist ya gurgunce tun lokacin da ɗan takararta François Hollande ya riƙe muƙamin shugaban ƙasa tsakanin 2012 zuwa 2017.
Masu sa ido sun ce Emmanuel Macron zai ci ribar ɓarakar ɓangaren masu ra'ayin kawo sauyi, yayin da kuma ɗaya ɓangaren ke zargin shi da kwaikwayon salon siyasarsu.
Yaƙin Ukraine ya ɗauke hankali kan yaƙin neman zaɓen ƴan takara, kuma shugaban ƙasa ya taka rawa ta diflomasiya.
Ya tsarin zaɓen ke aiki?
Za a gudanar da zaben zagaye na farko da na biyu mako biyu tsakani.

Idan har kamar yadda aka yi hasashe babu ɗan takarar da ya lashe sama da kashi 50 na yawan kuri'u a zagayen farko a ranar 10 ga Afrilu, ƴan takara biyu da ke da yawan ƙuri'u ne za su tafi zagaye na biyu wanda za a gudanar a ranar 24 ga Afrilu.
Duk wanda ya ci zagaye na biyu, shi za a rantsar a ranar 13 ga Mayu
Me kuri'un jin ra'ayin jama'a ke cewa?
Emmanuel Macron ne ke kan gaba a kuri'un jin ra'ayin jama'a aƙalla na watanni shida.
Ya ƙara zarra tun lokacin da Rasha ta abka wa Ukraine.
Marine Le Pen tana kan gaba fiye da sauran ƴan takara, a yayin da abokin hamayyarta Eric Zemmour, wanda ya taɓa cewa Vladimir Putin "yana burge shi," ya yi ƙasa

Mene ne manyan batutuwa?
Baya ga Ukraine, kuri'un jin ra'ayin jama'a sun nuna cewa manyan batutuwan su ne tattalin arziki da shige da fice da kuma tsaro.
A Janairu, Faransa ta wallafa ci gabanta mafi girma tsawon rabin ƙarni, inda ta farfaɗo daga tasirin annobar korona.

Ƙarfin tattalin arzikin Faransa zai yi tasiri ga yaƙin neman zaɓen Macron.
Faransa ta ga alƙalumman rashin aikin yi ya ragu zuwa kashi 7.4 kusan dab da alƙawalin da shugaban ya yi lokacin da ya hau kan mulki.
Kan batun shige da fice, alƙalumma sun nuna cewa a 2020 akwai baƙi miliyan 6.8 da ke zaune a Faransa.
Kusan kashi ɗaya bisa uku ƴan ƙasashen Turai ne daga ƙasasehn Tarayyar Turai da kuma waɗanda ba su cikin ƙungiyar.
Ƴan Algeria ne mafi yawa, sai ƴan Morocco da kuma ƴan Portugal.

Batun shige da fice ya fi mamaye yaƙin neman zaɓen ƴan takara masu ra'ayin riƙau.
Mr Zemmour ya yi alƙawalin aiwatar da "hana shige da fice" idan har ya ci zaɓe zai mayar da ƴan Algeria 100,000 gida da Tunisia da kuma Morocco.
Ms Le Pen na adawa da manufofinsa inda ta ce za ta yi zaɓen raba gardama kan rage kwararar baƙi idan har ta zama shugabar ƙasa.
Game da batun tsaro, Emmanuel Macron ya yi alƙawalin zuba dubban ƴan sanda a kan titi, bayan fuskantar suka daga Ms Pécresse da Mr Zemmour da Ms le Pen.
Mr Macron ya ce an samu raguwar aikata laifuka lokakcin mulkinsa
Faransa ta sha fara da hare-haren a shekarun baya wanda ya mayar da tsaro abu mai muhimmanci ga Faransawa.











