Zamantakewa: Me ya sa salon zance tsakanin saurayi da budurwa ya sauya?

Bayanan bidiyo, Bidiyon zamantakewa kan tsarin zance tsakanin samari da 'yan mata

Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.

A wannan kashi na 30 din, shirin ya yi duba ne kan abubuwan da suka sa salon zance tsakanin saurayi da budurwa ya sauya.

A wasu shekaru can baya da suka wuce, idan saurayi ya je zance wajen budurwarsa iyaye suna tabbatar da cewa an yi zancen nan a wurin da jama'ar gidan ke yawan wucewa ta wajen, wato waje mai yalkwar shige da ficen jama'a.

Sannan kuma sai an hada budurwar da 'yar rakiya.

Ni kaina na kan tuna lokacin da nake raka wasu yayyena hira, ta yadda zai yi wuya a shigo da wani abu marar kyau cikin lamarin.

Amma yanzu fa, yaya tsarin zance tsakanin samari da yan mata yake?

Batun da shirin zamanatakewa wannan makon ya duba kenan.

Wasu samari da dama da na ji ta bakinsu sun shaida min cewa a yanzu an fi yin zance a cikin mota, ko a tafi wajen shakatawa ko kuma wajen cin abinci.

"Gaskiya yanzu idan mu samari muka je zance ƴan matan ba sa fitowa da ƴan rakiya, duk da dai da ana hakan da zai fi tsari," in daya daga cikin samarin Arfat El-Nafaty.

Tirkashi, to a irin wannan salon a zancen zamani kenan abubuwa da dama na faruwa a zamantakewar samari da ‚yan mata da ka iya rusa al'umma ba tare da an bai wa lamarin muhimmanci ba.

Bari mu ji me zai sa iyaye su bar lamarin zance, wanda shi ne silar neman aure ya tabarbare haka ba tare da sa ido kamar yadda su aka yi musu a baya ba?

Hajiya Fatima Cikaire ta ce ita a ganinta sakacin iyaye ne ya jawo hakan.

Ta ce: "Da iyaye za su daure su dinga sa ido kan tsarin zancen ƴaƴansu daga mazan har matan da an samu sauƙi lalacewar lamurra."

A bayyane yake cewa in dai za a bar lamari irin na zance tsakanin saurayi da budurwa kara zube to abubuwa marasa dadi za su ci gaba da bullowa ta ko ina a fannin neman aure.

A cikin wannan shirin Sheikh Dakori, wani malamin addinin Musulunci ya ya matuƙr jan hankali a kan wannan lamari.

Wannan layi ne

Wasu shirye-shiryen na baya da za ku so

Wannan layi ne

Keta haddi

A yayin irin wannan salo na zancen wani da ya samu gangara sai ya zarme, ya nemi keta kyakkyawan mutuncinki da kika dade kina tanadi ke da iyayenki.

Don haka neke son bai wa 'ya'yan namu da kannemu mata wata satar amsa.

Kar ki yarda ko da wasa ki ba da kofar keta haddinki.

Namiji duk iskancinsa da iya shegensa za ki ji shi a majalisa yana ihun ai shi mace mai cikar mutunci yake so.

Kuma idan har kin ba shi fuska wani abu ya faru, can a teburin mai shayi dai zai baje kolin tozartaki, wani ma ko da bai kai ga keta mutuncin naki ba, wata kila a shan minti aka kare, to can za a tsinto shi yana yarfa maki sharri yana yo wannan ai na gama da ita.

Kai kuma saurayi dole ka tuna cewa kai uba ne, wa ne, miji ne, kaka ne, kuma kani ne, ko da ba yau ba nan gaba za ka zama.

To fa wataran duk wacce ka taba, rayuwa na iya juyowa kan naka ahalin a taba su.

Idan ka je zance ka guji tsalle-tsalle, ka nutsu ka yi abin da ya kai ka ba tare da keta haddi ba.

Ka yi hirarka cikin mutunci, ka ma dinga bukatar a taho maka da 'yan eye service din kamar yadda kuke kiran 'yan rakiyar.

Mu kuma iyaye lallai babban kalubalen duk a kanmu yake.

Dole mu dage da sa ido da bibiyar lamarin 'ya'yanmu da jan su a jiki, da nusar da su illolin hakan cikin dabara, ko don sauke hakkin tarbiyyarsu da aka dora mana.