Zamantakewa: Tarbiyyar mata da matasanmu a zamanin Tiktok
Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.
A wannan kashi na 27 din, shirin ya yi duba ne kan tarbiyyar mata da matasanmu a zamanin Tiktok
Ki yi hasashen cewa watarana kin wayi gari, sai ɗanki ko jikarki ta same ki ta ce Mama, kamar ke ce a wannan bidiyon ko?
Da kika duba sai kika ga wani tsohon bidiyo ne da kika wallafa a tiktok shekara 15 ko 20 da suka gabata.
A cikin bidiyon kina ta ƙunduma ashariya ko kina ta rawa da girgiza jiki, ko kina munana kalamai na batsa, ko kuma kina bin wata waƙa ta rashin mutunci kina murmushi (tare da taba wasu sassan jikinki).
Ko kuma kai ɗanka ko jikanka ya nuna maka irin dai wannan bidiyo kana wata baɗalar.
Idan kuna ga hakan tamkar almara ce to tabbas abin da ke shirin faruwa kenan nan da wasu shekaru masu zuwa. Don haka ku zauna cikin shiri.
Da zarar an ambaci Tiktok a wannan yankin namu, na tabbata ba abin da zai zo ranka sai irin dabdalar da ake yi a Sahar.
Daga zage-zage da ashariya, sai raye-raye da wasu abubuwan marasa dadin ji da ke faruwa tsakanin matasanmu maza da mata.
A baya irin wadannan abubuwan na faruwa ne tsakanin wasu tsirarun kawaye dake rigima tsakaninsu, ko kuma raye-raye a lokacin bukukuwa, to amma zuwan tiktok sai ya ba wa wadanda za a iya cewa ba su da dogon tunani damar fitowa tsakiyar kasuwa su yi wa kansu tonon solili da fito da ainihin tarbiyyarsu.
Wasu na baya da za ku so ku gani
Abin da ya fi bai wa mutune takaici shi ne shigar matan aure cikin irin wannan halayya, ba tare da duba martabar aure ba.
Hakan ya sa mutane irin su Lalilah Ali Othman wata fitacciya a shafukan sada zumunta suke ganin laifin mazansu ne, sannan su kuma matan a ganinta suna da ƙarancin tunani.
Da yake Hausawa na cewa Allah ɗaya gari bamban, yayin da masu amfani da tiktok a yankinmu ke sheƙe ayarsu a manhajar, su kuwa a can kasashen da suka ci gaba, matasansu sun duƙufa ne wajen ganin ta yaya za su samu taro da kwabo a Tikotok din, da kuma yin abubuwan da za su kawo musu ci gaba.
Kwanan nan ma wani bincike ya nuna cewa mutane na shafe kashi 1 cikin uku na lokacin da suke da shi a kowace rana ashafin TikTok.
Amma fa wasu masu amfani da sauran kafafen sada zumuntar ma irina tsoro da fargaba shiga tiktok muke yi. Ko za ka shiga sai dai ka yi shawagi ka fita, idan kuwa ka tsaya kallon ruwa to tabbas kwado zai yi maka kafa.
Ga ƴan jarida irina, dole watarana neman labarai ya kai mu tiktok. Sai dai dole mutum ya kasance mai taka tsantsan wajen amfani da manhajar.
Ƴan uwa musamman, ma 'yan uwana mata, kun dai ji shawarwarin da aka ba ku, mai yiwuwa idan kika yi duban tsanaki kika saurari shawarwarin da kunnen basira, su tserar da ke daga jin kunyar jikokinki ko 'ya'yanki ko ma surukanki.
Sannan za ta taimaka wajen rage tsuru-tsuru din da za ki yi idan aka yi miki tambayar da ba ki da amsar ta ko kuma kike jin kunyar ba da amsar ta, gami kuma da yi miki magananin nadamar da za ki iya yi a lokacin da ba ta da amfani.
Dadina da gobe saurin zuwa in ji masu magana. Sannan kuma akwai tsufa akwai kuma mutuwa. Wadannan su ne manyan abubuwan da aka jarrabi dan adam da su da ba su da magani.
Abin da zan kara a nan shi ne, ki guji biyewa masu saka challenge ana cewa ki aika bidiyonki kina rawa, sannan idan har kin ji cewa son rawa kike, to zai fi kyau ki kunna a dakinki ki cewa mijinki so kike ki masa rawa, ki danse son ranki, kai kuma oga ka daure ka hada da liki da kurantata kana cewa ya yi sarauniyar 'yan rawa ta duniya.
A wani makon, za mu yi duba ne kan zamantakewar agola a gidan uban riƙonsa.












