Zamantakewa: Me ya sa ake tsangwamar zawarawa a cikin al'umma?
Shirin na wannan makon maimaici ne na wanda muka yi na kashi na 16 ranar 16 ga watan Oktoban 2021.
Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.
A wannan kashi na 16, shirin ya yi duba ne kan yadda mu'amala take tsakanin zawarawa da al'umma.
Gyaran zamantakewa a cikin al'umma ya shafi dukkan fannonin rayuwa, ba sai na gidan aure da kawance da surukuta ba kawai.
Muzantawa ko bai wa kalmar bazawara wata ma'ana mara kyau ita ce tsangwama ta farko da 'ya mace da aurenta ya mutu ke fama da shi.
Shi ya sa wannan makon muka yanke shawarar tabo batun irin kallon da wasu al'umma ke yi wa matan da aurensu ya mutu.
Duk yadda ka kai ga jin zafin cewa wance na zawarci fa bai kai ga ita da abin ya shafa ba, don cikin 2 akwai daya, walau dai ta fi ku jin takaicin mutuwar auren nata, ko kuma auren ya yi munin da gara mata zama a haka maimakonsa.
Wannan kuma zaɓinta ne ba naku ba, rayuwarta ce ba taku ba.
A hirar da na yi da mata da dama da aurensu ya mutu, sun gaya min rashin jin dadinsu kan yadda ake yi musu wani kallo na daban a cikin al'umma.
Bara'atu Aliyu wata ma'aikaciya ce a Abuja da kaddarar mutuwar aure ta fada mata, kuma ta ce min akwai abubuwa da dama da ake dangantawa zawarawa marasa da di.
"Wasu lokutan ki ga ana tsangwamarmu ana cewa da gangan muka kashe auren don kawai mu yi duniyancinmu, bayan kuma ba haka ba ne.
"Sannan a wasu lokutan har kawaye ma sai su dinga gudunka ana nuna kamar kina son kwace musu mazaje ne. Saboda Allah kawai don ka hadu da kaddarar aure sai kuma kowa ya dinga zaton nasa mijin za ka aure?" in ji Bara'atu.

Wasu na baya da za ku so ku karanta

Ta ce a wasu lokutan irin wannan tsangwama kan sanya mace fadawa cikin lalurar tsananin damuwa har abin ya kai ta ga yin gaggawar wani auren ba tare da bincike ba.
"A karshe kuma sai a je a sake wani auren na gaggawa da za a kasa zaman lafiya a sake fitowa, wannan din sai ya sa a sakata a jerin wadanda ba sa son zaman aure, bayan tun farko tsangwamar ce ta kai ta wannan yanayi.
Kowanne fanni na lamarin zamantakewa na nan shimfide cikin dokokin addini, wannan ne ya sa muka tuntubi Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa don jin yadda ya kamata a kyautata zamantakewa tsakanin al'umma da zawarawa.
Ya ce bai kamata a tsangwami mace kawai don wata kaddara ta afka mata ba, kamata ya yi a ja su a jiki a
Don gudun jawowa kai abin magana, su ma matan da aurensu ya mutu din da ake tsangwama ko wane irin taku ya kamata su yi don hana ba da ƙofa na yin maganganun banza a kansu?
Malam ya bai wa su ma matan shawara cewa su zama masu kamun kai da ƙin shiga abin da ba ruwansu, tare da tsare mutuncinsu.
Ita ma Bara'atu maganar da ta yi kenan, cewa idan dai kika iya takunki na yin kaffa-kaffa da taka tsantsan da rayuwa, to masu tsangwamar ma za su yi su bari.
Masu magana sun ce, "kowa ya iya allonsa ya wanke."

Ƙarin wasu da za ku so













