Zamantakewa: Me ya sa wani lokacin kishin faccaloli ya fi na kishiyoyi zafi?

Bayanan bidiyo, Matakan gyara zamantakewar matar wa da matar ƙani

Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.

A wannan kashina bakwai, shirin ya yi duba ne kan taɓarɓarewar zamantakewar faccaloli, wato matar wa da ƙani, da kuma yadda za a gyara mu'amalar.

Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.

A wannan kashi na bakwai din, shirin ya yi duba ne kan kan taɓarɓarewar zamantakewar faccaloli, wato matar wa da ƙani, da kuma yadda za a gyara mu'amalar.

Babu wani abu da ya fi ba da mamaki a rashin jituwa ko saɓani na zamantakewa irin lamarin faccalanci ko kishin balbali kamar yadda wasu ke kiransa.

Wannan satin batun da za mu duba kenan bayan rufe babin surukuta.

Faccala na nufin matar wa ko ƙanin miji, a wasu wuraren ana kiran zaman da Kishin Balbali ko Kishin Sauri.

A kan dace a wasu iyalan a samu fahimtar juna tsakaninsu, amma a mafi yawan gidaje na al'ummarmu kishi ake bugawa a tsakani, har ma ka rasa dalilin yin hakan.

To ai dole a rasa dalili, mace mijinta daban naki daban, ƙaddarar kowa daban, amma sai a dinga rigima kamar ba gobe?

Babbar matsalar ma ita ce sai fadan a wasu lokutan ya koma tsakanin mazajen da suke 'yan uwan juna ko kuma 'ya'ya su taso da ƙiyayyar juna a tsakaninsu.

Na sha ganin gidajen da kishin sauri ya zama gagarumar matsala, ya jawo baƙar gaba har ma abin ya shafi mazajen nasu zumuncin ya taɓarɓare.

Wannan layi ne
Wannan layi ne

Sai dai wani abin sha'awa shi ne, akwai dubban faccaloli da suka haɗa kansu suke zaune lafiya ba tare da ka-ce na-ce ba. Hakan ya yauƙaƙa zumuncinsu da na mazajensu da na ƴaƴansu.

Kuma sun cimma haka ne ta hanyar kawar da kai daga ƙananan matsaloli da girmama juna da kiyaye abin da ka je ya zo.

Cikin mutanen da na yi hira da su a wannan makon, har da wasu faccalolin juna uku da suke tare fiye da shekara 10, sun kuma ce min ko sa in sa ba su taɓa yi ba.

Hajiya Jamila Bebeji na ɗaya daga cikinsu, ta kuma ce gidan suurkanta gida ne mai yawan faccaloli amma tun da ta shiga cikinsa lafiya lau suke zaune babu gutsuri tsoma balle mugun kishi.

"Kowaccenmu ta san matsayinta, matar ƙani na ganin girman matar wa, ita ma matar wa tana ƙoƙarin yin adalci a matan ƙannen mijinta.

"Muna taimakekeniya a tsakaninmu, sannan komai za mu yi tare muke yi, muna yawan tuntuɓar juna, muna kuma ƙoƙarin haɗa kan mazajenmu da ƴaƴanmu," a cewarta.

Ita ma ɗaya daga cikin faccalolin Hajiya Bebeji ta ce, "har mamakin faccalolin da ke kishin juna nake yi.

"Mu a gidanmu ina iya ɗaukar ƴaƴana na kai su gidan ɗan uwan mijina idan tafiya ta kama ni, kuma za a riƙe min su tamkar ni da babansu muna nan.

"To ba komai ya kawo hakan ba sai zaman lafiya da fahimta," in ji ta.

Wannan layi ne

Mazan ma suna da rawar takawa a wannan gaɓar, kamar yadda Shehu Abdul'aziz wani mai shatrhi kan zamantekwa ya shaida min.

Ya gaya min muhimman abubuwa biyar da ya kamata maza su kiyaye:

  • Na farko a sanya tsoron Allah a zuƙata. Kar a matsayinka na namiji ka zama kai ne mai tunzura matarka ta yi wa ɗan uwanka da matarsa rashin mutunci.
  • Na biyu dole mazajen kowa ya san matsayinsa. Yaya ya rike girmansa ƙanin ya kama kansa.
  • Na uku kar mazan su yarda matan su san tsakaninsu da ƴan uwansu.
  • " Idan kana da matsala da ɗan uwanka kar ka tattauna ta da matarka, don kuwa hakan na iya ta'aazara ya koma tsakanin matanku, su kuwa ba lallai su sasanta ba sai dai abin ya ƙara zafafa," a cewarsa.
  • "Kar ku yarda matanku su san sirrinku, hakan zai sa matarka ba za ta ga darajar ɗan uwanka ba balle ta ga na matarsa.
  • Na huɗu ya ce kar a zauna gida ɗaya ko unguwa ɗaya idan da hali, don daga nan ne babbar matsala ke farowa.
  • Sai na ƙarshe idan matsala ta taso a tsakaninsu to a zauna a gano bakin zaren sannan a yi sulhu.

Ni kuma na ƙara da cewa idan mijin waccar ya fi naki arziki da wadata ne, to ke ma dinga tuna wasu alkhairai komai ƙanƙantarsu na mijinki da zai sa ki ga ai kin dace ta wasu wuraren, ba kudi ne kawai nutsuwar zuciya ba

A tsarkake zukata, kar ki dasa wa kanki hassada da kyashin wance don kawai kin ga wasu nasararori baibaye da ita, ki dinga duba ke ma nasu nasarorin komai rashin yawansu don kuwa a hakan ma watakila kin fi waccar bacci da saleba

'Yan uwa mata masu faccaloli, da fatan wadannan shawarwari sun muku amfani, ku kwantar da hankulanku ku zauna lafiya da juna, don masu iya magana kan ce, wata rana sai labari, mai ba dsa labarin ma wata rana baya nan.

Shiri na gaba na zamantakewa zai yi duba ne a kan batun rikon 'ya'ya. Sai ku biyo mu.

Wannan layi ne