Zamantakewa: Yadda mu'amala take tsakanin ƴan aiki da iyayen gidansu

Bayanan bidiyo, Zamantakewa: Yadda mu'amala take tsakanin 'yan aiki da iyayen gidansu

Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.

A wannan kashi na 15, shirin ya yi duba ne kan yadda mu'amala take tsakanin ƴan aiki da iyayen gidansu.

Na san wasu da dama za su ce ita kuma Halima me ya kai ta taɓo batun zama da ƴan aiki.

A ganinsu wataƙila ƴar aiki ba ta da ƙimar da za a tattauana batun yadda za a kyautata zamantakewa da ita.

Ni ko a ganina duk wacce kika dauka ta kika sanya ta a cikin iyalanki, a kawana tare a tashi tare, ai tana ɗaya daga cikin muhimman mutanen da ya kamata ki iya zama da ita, ko don gudun cutuwa.

Na shan jin matsaloli kan ain da ya shafi 'yan aiki, kwanaki na yi wani ƙaramin bicnke kan yawan ƴan aikin da mata ke yi inda na gano cewa wasu kan sauya ƴan aiki ne kusan duk shekara kamar dai yadda ake yaye ɗailban makaranta.

Wataƙila saboda ba sa dacewa da ƴan aiki na gari ko kuma su nasu halayen ke korar ƴan aikin. Ko ma dai mene ne, lallai akwai bukatar daga ƴan aikin har iayyen gida kowa ya san matsayinsa.

A wasu gidajen a kan samu cewa ƴan aiki ne marasa kirkin ta yadda har za su gallabi matar gida da ma sauran mutanen gida, su zame musu ƙayar maƙogoro, yayin da a wasu wuraren kuma iyayen gidan ne masu muzgunawa ƴan aiki da mayar da su ba bakin komai ba.

Wannan layi ne

Wasu na baya da za ku so ku karanta

Wannan layi ne

Na yi hira da mata da dama da suka ce min su manyan halaye na gari da suka fi buƙata daga ƴan aikinsu ba su wuce amana da gaskiya da kyautatawa ba.

Su kuma ƴan aiki da na ji ta bakinsu sun ce babu abin da suka fi tsana irin wulaƙanci da muzantawa.

Kenan ya kamata iyayen gida su daure su zama adilai, masu kyautatawa, masu tausayi, sannan su dinga sa ido kan mu'amalar ƴan aiki da ƴaƴansu har ma da mazajensu, ba ma son tsinto ki a intanet kina wayyo na bonu na lalace ƴar aiki ta aure min miji.

Ku kuma yan aiki, na san zamani ya zo da kuke da wayoyi kuma ku ke iya sa data, don haka na san kuna kallona.

Ku zama masu rikon amanar da aka ba ku, ban da gulma da haɗa waje, ban da shiga abin da ba a saku ba, ku san iyakarku a cikin gida, ba ruwanku da zaƙewa da wuce gona da iri.

Wannan layi ne

Ƙarin wasu da za ku so

Wannan layi ne