Zamantakewa: Yadda uwar miji za ta ja girmanta a idon suruka
Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.
A wannan kashina shida, shirin ya yi duba ne kan yadda uwar miji za ta ja girmanta a idon suruka.
Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.
A wannan kashi na shida din, shirin ya yi duba ne kan alakar uwar miji da surukarra. Wato dai irin yadda wasu uwayen mijin ke gallazawa matan 'ya'yansu ba gaira ba dalili.
A makon da ya gabata mun yi duba ne kan yadda wasu matan kan dauki kishi da tsana su dora kan uwar mijinsu.
A matsayinki na uwar miji tun farko ya kamata ki bude zuciyarka ki karbi matar danki tun da shi ya zabe ta a matsayin abokiyar rayuwa.
Irin kulawar da za ki bai wa 'ya'yanki mata da shi dan naki, to irin ta ya kamata ki bai wa matar danki.
Ki kama girmanki kar ki nuna mata kina kishinta ko tsanarta, don yin hakan zai iya jawo maki raini.
Ya kamata a matsayinki ta uwa ki dinga dauke ido daga kan al'umuran gidan danki da na matarsa, hakan zai ba ki nutsuwar zuciya da salama.


Sai dai inda kika ga suna kauce layi, to a nan kina iya hada su ki tsawatar ba tare da nuna tsananin jin zafi ba.
A lokuta da dama a kan samu wasu iyayen mijin da biye wa 'ya'yansu da aka fi kora da kannen miji, a hadu a dibga muzgunawa matar dan'uwan.
Gaskiya a matsayinki ta babba bai kamata a samu hannunki a cikin wannan aika-aika ba.
Ki zama mai yawan yi mata alheri da son 'ya'yanta wadanda dama jikokinki ne. Kar ki nuna bambancin tsakanin jikokin 'ya'yanki mata da na mazan.
Kar ki ba da fuskar da za a dinga kawo miki maganganu da tsegumi a kan surukarki.
A duk lokacin da aka kawo miki irin wadannan zantukan sai ki yi kokari ki yi watsi da su da nuna ba kya son ji.
Kar ki zama mai yawan son jin halin da danki ke ciki da matarsa. Don idan kika ba shi dama yana yawan kawo maki korafi to hakan zai iya dasa miki tsanarta a ranki.
Shirin na wannan mako ya tattauna da wani malamin addinin Musulunci Sheikh Gwani Adam Alkali da kuma Malama Halima Sani.
Sai ku kalli bidiyon da ke can sama don jin nasu shawarwari da suka bayar na yadda za a gyara wannan zama na suruka da matar danta.












