Matan Saudiyya 28,000 na neman aikin zama matukan jiragen kasa

Asalin hoton, Getty Images
Mata 28,000 ne suka nemi ayyuka na gurabai 30 da suka danganci tukin jiragen kasa a Saudiyya - yayin da kasar ke kokarin sake bude sabbin hanyoyin da za su haɓaka rayuwar mata da saka su kan tsarin aikin yi.
Wani tallan samar da guraban ayyuka 30 ga ƙwararrun direbobin jiragen ƙasa mata a kasar ta Saudiyya ne ya janyo hankulan yawan waɗannan matan masu neman aikin.
Hakan na nuni da yawan bukatar hakan a yayin da kasar mai "ra'ayin mazan jiya" sassauta wasu daga cikin dokokinta kan ɗaukar mata aiki.
A shekara ta 2018 aka ƙaddamar da layin dogon jiragen kasa masu gudun gaske tsakanin Makka da Madina - kuma ana sa ran jiragen su soma aiki a tsakiyar wata mai kamawa.
Kuma a wannan lokacin ne kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa Renfe na kasar Sifaniya ya yi kokarin tantance dubban takardun aiki da matan na Saudiya da suka aike na zama direbobi ko matuka jiragen.
Kamfanin na Renfe ya bayyana cewa bayar da fifiko ga wadanda suka fi ƙwarewa a Turancin Ingilishi a tantance masu neman aikin da ya yi ta shafin intanet, ya taimaka masa wajen zaftare yawan wadanda suka rubuta neman aikin da kusan rabi.
Ya kuma ce zai ci gaba da hakan har ya zuwa cikin watan Maris.
Yawan mata ma'aikata a fannin sufurin Saudiyya
Mata 30 din da kamfanin na Renfe ya fara dauka za su riƙa tuƙa jirage masu tsananin gudu daga tsakanin birnin Makka zuwa Madina bayan shafe shekara daya ana horarwar da ake biya.
Alkaluma na nuna cewa kashi ɗaya cikin uku na mutanen da ake ɗauka aiki yanzu a kasar mata ne - adadin ya ruɓanya idan aka kwatanta da shekaru biyar baya.
Ayyukan da a baya ake keɓewa don maza zalla yanzu haka ana bai wa mata dama.

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai har yanzu rashin aikin yi na mataki na ƙololuwa a kasar tsakanin matasa - musamman mata ma.
Amma kuma tsare-tsare da buririka habbakar tattalin arziki na kasar ta sanya gaba na iya taimakawa wajen sake samar da gurabe sabbin ayyuka a fanoni da dama, har da yawon bude ido.
Tururuwa ko yawan takardun da aka karba na mata na nuna irin zakuwa da mata ke da shi na ganin su samu dama a kasar, wanda kwana-kwanan ake sausautawa mata damar samun ayyukan yi.
A baya dai samun damar guraban aiki ga matan kasar Saudiyya ya tsaya ne a kan aiki a matsayin malaman makaranta, da ma'aikatan kiwon lafiya, saboda dole su rika tsauraran dokokin keɓe jinsi.
An haramta wa mata tuka mota a kasar ta Saudiyya, har sai ya zuwa shekarar 2018.
A cikin shekaru biyar da suka gabata yawan mata ma'aikata ya karu da kashi 33 bisa dari a daidai lokacin da Yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya ya fito ya yi bayani a madadin masarautar kan fadada hanyoyin bunkasa tattalin arziki.
Don haka yanzu mata na kama ayyukan da a baya maza ne da kuma baki 'yan kasashen waje kawai aka amince wa yi a kasar.
Amma kuma har yanzu alkaluman adadin mata ma'aikata a kasar rabin adadin na mazan ne a cikin watan Afrilu zuwa Satumbar shekarar 2021 a kashi 34 da digo daya bisa dari, kana rashin aikin yi a tsakanin mata ya ninka har sau uku fiye da na mazan mai kashi 21 da digo dara bisa dari.











