Hotunan bikin fina-finai karon farko a Saudiyya

Wasu hotunan bikin fina-finai karon farko a Saudiyya

Bajekolin fina-finai a Saudiyya

Asalin hoton, AFP PHOTO /RED SEA FILM FESTIVAL

An buɗe bikin fina-finai na farko a ƙasar Saudiyya a birnin Jeddah - kasa da shekaru hudu da ɗage haramcin nuna fina-finai a ƙasar.

Bikin fina-finai a ƙasar, wanda aka soma ranar Litinin da daddare, zai gudana ne tsawon kwanaki 10 inda za nuna fina-finai 138 daga sassan duniya.

Wannan ne karon farko da ake yin bikin nuna fina-finai na duniya a Saudiyya, wanda fitattun taurarin fina-finan duniya suke halarta.

Za a karrama darakta mace ta farko a Saudiyya Haifa al-Mansour - wacce ta fara fim din Wadjda da ta lashe kyauta.

Manufar bikin ita ce bunƙasa masana'antar fina-finai a ƙasar Saudiyya - ta fuskar shirya fina-finai da kuma kasuwarsu da nunawa a sinima da aka buɗe tun shekarar 2018.

Bajekolin fina-finai a Saudiyya

Asalin hoton, AFP PHOTO /RED SEA FILM FESTIVAL

Bajekolin fina-finai a Saudiyya

Asalin hoton, AFP PHOTO /RED SEA FILM FESTIVAL

Bajekolin fina-finai a Saudiyya

Asalin hoton, AFP PHOTO /RED SEA FILM FESTIVAL

Bajekolin fina-finai a Saudiyya

Asalin hoton, AFP PHOTO /RED SEA FILM FESTIVAL

Bajekolin fina-finai a Saudiyya

Asalin hoton, AFP PHOTO /RED SEA FILM FESTIVAL

Bajekolin fina-finai a Saudiyya

Asalin hoton, OTHER

Bajekolin fina-finai a Saudiyya

Asalin hoton, AFP PHOTO /RED SEA FILM FESTIVAL