Yadda minista ya yi iyon sa'a 12 bayan jirgin samansa ya fada cikin teku

Serge Gelle

Asalin hoton, Twitter

Bayanan hoto, Ministan 'yan sandan Madagascar

Wani ministan gwamnatin Madagascar ya ce ya yi iyo na tsawon sa'a 12 domin tsira da ransa, bayan da jirginsa mai saukar ungulu ya fada a cikin teku yayin wani aikin ceto da yake jagoranta.

"Lokaci na bai yi da zan mutu ba," in ji ministan 'yan sanda Serge Gelle a gajiye a lokacin da yake murmurewa a kan gadon da ake daukar marasa lafiya.

Wasu jami'an tsaro biyu ma da ke tafiya tare da shi a cikin jirgin sun tsira da rayukansu.

Tawagar ta dade tana duba wani yanki da ke arewa maso gabashin kasar inda wani jirgin fasinja ya nutse.

Akalla mutane 39 ne suka rasa rayukanu a wannan hatsarin, kamar yadda jami'ai suka bayyana a ranar Talata.

A shafinsa na Twitter, shugaban kasar Andry Rajoelina ya nuna alhininsa kan wadanda suka mutu sannan kuma ya jinjinawa Mista Gelle da sauran jami'an biyu, wadanda suka isa garin Mahambo da ke gabar teku daban.

Ba a san abinda ya janyo hatsarin na ranar Litinin ba amma Mista Gelle, mai shekaru 57, ya ce bayan hadarin ya yi iyo daga "7:30 na daren Litinin, zuwa karfe 7:30 na safiyar Talata," zuwa Mahambo.

Ya ce bai samu rauni ba amma ya ce yana jin sanyi.

"Ina so ku yadda wannan bidiyon don 'yan uwa su gani, abokan aikina su gani, 'jami'an gwamnati su gani. Ina nan a raye kuma cikin koshin lafiya," Mista Gelle ya shaida wa mazauna kauyen Mahambo.

Shugaban 'yan sanda Zafisambatra Ravoavy ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Mista Gelle ya yi amfani da daya daga cikin kujerun jirage masu saukar ungulu a matsayin madafa.

Mista Ravoavy ya ce "Kodayaushe jarumi a harkar wasanni, kuma ya ci gaba da yin haka a matsayinsa na minista, kamar dai dan shekara 30 ... yana da jijiyoyi na karfe," in ji Mista Ravoavy.

Mista Gelle dai ya shafe shekaru 30 yana aikin 'yan sanda kafin a nada shi minista a watan Agusta.