Ana ci gaba da aikin gano mutanen da jirgin ruwa ya kife da su a Bagwai

Asalin hoton, ALIHU TANKO YAKASAI
Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta sanar da hana amfani da jirgin ruwan fasinja a karamar hukumar Bagwai.
Hukumomin sun dauki matakin ne a zaman majalisar zartarwa na jiya Laraba, kwana daya bayan hadarin jirgin ruwa na ranar Talata da ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dama.
Da yake yi wa BBC karin bayani dangane da matakin haramta amfani da kwale-kwalen a Bagwai, kwamishinan yada labarai na jihar Kano Muhammad Garba, ya ce "gwamnatin jihar ta samar da motoci kirar bas guda biyu don jigilar mutane kyauta, daga hayin Badau zuwa garin na Bagwai.
Ya kara da cewa " za a ci gaba da jigilar ta mota har zuwa lokacin da za a samar da sabbin kwale-kwale ga al'umma."
Majalisar zartarwar ta kuma sanar da cewa yayin da ake kokarin samar wa al'ummar Bagwai da wata hanyar sufurin, kwamitin na musamman zai fara aikin gano musabbabin kifewar jirgin.
Ba wannan ne karon farko ba da ake samun hatsarin jirgi a karamar hukumar ta Bagwai.
A watan Afrilun 2008 ma mutun 40 sun mutu, a lokacin da jirgin wani ayarin yan biki da ke kan hanyarsu ta kai Amarya daga hayin Badau na Bagwai ya kife.
A wata mai kama da haka Shugaba Muhammadu Buhari ya jajanta wa jama'ar jihar Kano, musamman iyalan sama da mutum 20 aka bayar da rahoton mutuwarsu kawo yanzu.
A wani saƙo da ya aike wa gwamnatin da jama'ar jihar, shugaban ya ce duka hukumomin gwamnatin tarayya za su cigaba da bayar da gudunmawar da ta dace a daidai lokacin da ake ci gaba da neman waɗanda suka ɓace.
A ranar Talata ne hatsarin ya faru, kuma yawancin fasinjojin da lamarin ya rutsa da su yara ne ƙanana ɗaliban Islamiyya.
Jami'an ƴan sanda da ƴan kwana-kwana da masunta ne ke ci gaba da aikin ceton tun bayan faruwar lamarin.
Da wannan safiyar ta Alhamis za a ci gaba da neman ragowar gawawwakin mutum 12 da ba a iya ganowa ba jiya Laraba.











