Waiwaye: Neman gafarar Sarki Sanusi, Naɗa Alaramma kwamishina a Kano
Kamar kowane mako, a yau ma mun yi waiwaiye kan muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata tun daga Lahadi 28 ga watan Nuwambar 2021 zuwa Asabar 05 ga watan Disamba.
Yadda kotu ta ruguza zaben bangaren Ganduje na jam'iyyar APC

Asalin hoton, Kano State Government
A makon da ya gabata ne wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da aka yi wa Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam'iyyar APC na jihar da ma dukkan shugabannin da bangaren Ganduje ya gudanar.
Kazalika kotun ta ce bangaren shugabannin da aka zaba a bangaren Sanata Malam Ibrahim Shekarau su ne halastattun shugabannin APC na jihar.
Da ma dai ana takun-saka tsakanin bangaren Ganduje da na Shekarau kan shugabancin jam'iyyar ta APC.
Kotu ta umarci gwamnatin Ganduje ta nemi gafarar Muhammadu Sanusi II

Asalin hoton, @SARKINKANO_SUNUSI_FANS_
Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, babban birnin Najeriya ta umarci babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari'a na Jihar Kano da ke arewacin kasar ya nemi gafarar tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II bisa korarsa daga jihar.
A zaman kotun na ranar Talata, mai shari'a Anwuli Chikere, ta ce korar da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yi wa tsohon sarkin na Kano daga jihar "haramtacciya ce kuma ta saba wa kundin tsarin mulkin" Najeriya.
Kotun ta umarci kwamishinan shari'ar na Kano ya wallafa neman gafarar a jaridu biyu na kasar.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, ya ruwaito mai shari'a Chikere tana cewa dokar majalisar sarakunan Kano ta 2019 wadda Gwamna Ganduje ya yi amfani da ita wajen korar tsohon sarkin daga jihar bayan an sauke shi daga kan sarauta ta saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.
Hatsarin jirgin ruwan Bagwai

Asalin hoton, Getty Images
A makon da ya gabata ne aka yi hatsarin jirgin ruwa a Ƙaramar Hukumar Bagwai a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Waɗanda hatsarin ya rutsa da su akasarinsu ƙananan yara ne kuma ƴan Islamiyya.
Rahotannin sun ce fiye da mutum 30 ne ake tunanin sun ɓata bayan hatsarin kwale-kwalen.
Bayanai sun nuna cewa mutanen sun taso ne daga ƙauyen Badau zuwa garin Bagwai domin yin Maulidi amma kwale-kwalen ya nutse da su.
Rundunar 'yan sandan jihar ta ce kwale-kwalen yana dauke ne da mutum kusan 50.
Yan majalisa sun gayyaci Shugaban INEC kan zaben fidda gwani

Asalin hoton, Getty Images
A makon da ya gabata ne majalisar wakilai a Najeriya ta gayyaci shugaban hukumar zaben kasar da ya je gabanta ya yi bayani a kan kudin da za a kashe a kan zaben fid da gwani na ƴar tinke, wanda dama ke cikin sabuwar dokar zaben da ƴan majalisar suka zartar kwanan nan.
Batun zaben fid da gwanin ya janyo ka-ce-na-ce a Najeriya, kasancewar gwamnonin jihohi suna adawa da tsarin ƴar tinken, yayin da ƴan majalisa ke cewa shi ne ya fi dacewa.
Ƴan majalisar wakilan sun amince da aika wa shugaban hukumar zaben kasar, Farfesa Mahmud Yakubu goron gayyata ne, bayan dan majalisar daga jihar Kogi, Honorabul Leke Abejide ya gabatar da kudurin a jerin batutuwa masu bukatar kulawar gaggawa.
Ƴan majalisar sun ce suna jin ana cewa zaben fid da gwanin kadai idan jam'iyyun siyasar kasar za su yi shi kai-tsaye, to zai lashe fiye da naira biliyan 500.
Ganduje ya naɗa Alaramma Ahmad Sulaiman kwamishina

Asalin hoton, Ahmad Sulaiman Ibrahim
A makon da ya gabata ne Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Alaramma Ahmed Sulaiman kwamishina na biyu a hukumar kula da makarantun firamare ta jihar Kano.
Alaramma Ahmad Sulaiman ne ya tabbatar da ba shi wannan muƙamin a saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya yi godiya ga gwamnan.
Ya wallafa hotunansa tare da gwamnan, a gefe akwai Sheikh Abdullahi Bala Lau wanda shi ne shugaban ƙungiyar Izala, da kuma sakataren ƙungiyar na ƙasa Sheikh Kabir Gombe.
Malam Ahmad Sulaiman ya roƙi Allah Ya sa albarka a kujerar da ya samu da kuma roƙon addu'ar jama'a kan taya shi riƙo.











