Kotu ta umarci gwamnatin Ganduje ta nemi gafarar Muhammadu Sanusi II

Asalin hoton, @sarkinkano_sunusi_fans_
Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, babban birnin Najeriya ta umarci antoni-janar na gwamnatin Kano da ke arewacin kasar ya nemi gafarar tsohon Sarki Kano Muhammadu Sanusi na II bisa korarsa daga jihar.
A zaman kotun na ranar Talata, alkaliyar kotun mai shari'a Anwuli Chikere, ta ce korar da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yi wa tsohon Sarkin na Kano daga jihar "haramtacciya ce kuma ta saba wa kundin tsarin mulkin" Najeriya.
Kotun ta umarci antoni-janar na gwamnatin jihar ta Kano ya wallafa neman gafarar a jaridu biyu na kasar.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, ya rawaito mai shari'a Chikere tana cewa dokar majalisar sarakunan Kano ta 2019 wadda Gwamna Ganduje ya yi amfani da ita wajen korar tsohon sarkin daga jihar bayan an sauke shi daga kan sarauta ta saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.
A cewar mai shari'a Chikere, kundin tsarin mulkin kasar "shi ne gaba a kan kowacce doka" kuma duk abin da ya ci karo da shi ya haramta.
A ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2020 ne gwamnatin jihar Kano ta sauke Muhammadu Sanusi na II daga kan mulki saboda zarginsa da "nuna rashin biyayya ga dokokin jihar Kano."
Daga nan ne gwamnatin ta dauke shi a jirgin sama zuwa kauyen Loko da ke jihar Nasarawa. Sai dai daga bisani an mayar da shi zuwa garin Awe duk dai a cikin jihar Nasarawan
Amma tsohon sarkin ya kai karar antoni-janar na gwamnatin jihar Kano da babban sufeton 'yan sandan Najeriya da darakta janar na hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS da kuma antoni-janar na tarayya bisa korarsa daga jihar.
Muhammadu Sanusi na II bai kalubalanci sauke shi daga kan mulki ba, amma ya nemi kotun ta bayar da umarni a sake shi daga tsarewar da aka yi masa a wancan lokacin da kuma dawo masa da 'yancinsa na kasancewarsa dan adam.
Kazalika ya kotu ta hana wadanda ya kai kara tsangwamarsa da kuma keta hakkinsa na dan adam.
Alkaliyar kotun tarayyar ta nemi gwamnatin Ganduje da wasu daga cikin mutanen da tsohon sarkin ya kai kara su biya Muhammadu Sanusi na II diyyar naira miliyan 10 bisa korarsa daga jihar ta Kano.












