Ganduje ne ya bukaci na karbi Sarki Sanusi na II - Gwamnan Nasarawa

Asalin hoton, Twitter/Nassarawa government
Gwamnan jihar Nassarawa da ke Najeriya, Abdullahi Sule, ya ce takwaransa na jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya kira shi a wayar tarho inda ya bukaci ya amince a kai tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II can idan an sauke shi daga kan mulki.
Ranar Litinin din makon jiya ne gwamnatin Kano ta sauke sarkin daga gadon sarauta bayan ta zarge shi da laifin kin yi wa hukumomi biyayya.
A ranar ce kuma aka dauke shi a jirgin mai saukar ungulu zuwa kauyen Loko da ke jihar Nasarawa inda ya kwana daya, ko da yake washe gari an mayar da shi garin Awe na jihar ta Nassarawa.
Jaridar Daily Trust ta ambato Gwamna Sule yana shaida wa wasu 'yan jarida cewa: "Jim kadan bayan an sauke shi [Sanusi na II], gwamnan Kano ya kira ni inda ya ce 'yanzu muka sauke Sarki kuma muna tunanin kawo shi jihar Nasarawa; Idan za ka amince ka karbe shi. Na shaida masa cewa zan yi matukar farin ciki na karbe shi."
Batun kai tsohon sarkin jihar Nasarawa dai ya jawo ce-ce-ku-ce inda kungiyoyi da jama'a daban-daban suka ce gwamnati ba ta da hurumin tura shi gudun hijira bayan ta sauke shi.
Lauyoyin Sarki Sanusi na II sun gurfanar da jami'an tsaro da gwamnatin jihar Kano a gaban kotu, wacce ta yanke hukuncin sakin sarkin da ba shi damar zama a duk inda yake so.
Tsohon sarkin ya bar jihar Nasarawa ne zuwa Lagos bayan ya yi ratse a birnin Abuja.

Asalin hoton, EL-Rufa'i Twitter






