Majalisar Dokokin Poland ta yi watsi da kudurin dokar hana zubar da ciki

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar dokokin Poland ta yi watsi da gagarumin rinjaye wani kudurin doka da ke neman sanya dokar hana zubar da ciki ko a wane hali tare da yanke wa matan da suka zubar da juna biyu hukuncin zaman gidan sarka na rai da rai.
Ita dai Poland daman ta kasance kasar da a Turai take da daya daga cikin tsauraran dokoki na zubar da ciki.
Ana ba wa mace damar zubar da ciki ne idan ya kasance an yi mata fyade ko wani makusancinta ne ya yi mata cikin, ko kuma juna biyun na barazana ga rayuwarta a matsayin uwa.
Kafin kaiwa ga matakin majalisar dokokin na daukar matakin watsi da kudurin dokar, sai da aka samu ce-ce-ku-ce a zauren majalisar.
Bayan an hau sama ne sai kuma aka sakko inda dukkanin manyan jam'iyyun kasar ta Poland suka yi watsi da kudurin.
Wasu daga cikin 'yan majalisar na bangaren hamayya cewa suka yi abin takaici ne har ma da aka yarda kudurin dokar ya samu damar kaiwa ga matakin karatun farko.
Wata mai magana da yawun jam'iyya mai mulki ta Law and Justice, jam'iyyar da ta goyi bayan tsaurara dokokin zubar da ciki na kasar a shekarar da ta wuce ta 2020, dokar da ta jawo gagarumar zanga-zanga, ta ce daure mata a kan dalilin zubar da cikinsu abu ne da ba za a lamunta da shi ba.
Kuma ta ce hakan zai kasance tamkar wani tukuici ne ga kungiyoyin masu goyon bayan zubar da ciki.
A shekarar da ta wuce a lokacin da Cocin Katolika ta kasar ta sa gwamnati ta sanya waccan doka ta kusan haramta zubar da cikin gaba daya a ranar 22 ga watan Oktoba na 2020, tare da wasu matakan domin karfafa wa jama'a gwuiwa su haifi yara.
Zanga-zangar gama-gari wadda ba a taba ganin irinta ba a kasar tun bayan rugujewar tsarin Kwaminisanci ta barke a fadin kasar a lokacin.

Asalin hoton, Getty Images
Haka kuma a 'yan watannin nan, mutuwar wata mata mai shekara 30 ta tayar da hankalin al'ummar kasar, har suka kara bazama wata zanga-zangar ta kasa gaba daya.
Ana daukar matar wadda aka santa da suna Izabel, kawai a matsayin ta farko da ta rasu a sanadiyyar sabuwar dokar ta Poland, abin da kuma wasu ke fargabar cewa wasu matan ma za su iya rasa rayukansu.
A watan Satumba ne, matar ta rasu sakamakon fargaba da ta samu bayan da likitoci suka ki cire mata dan tayin da ke cikinta, wanda aka gano yana dauke da wata nakasa.
A watan Nuwamba da ya gabata ne bayan da labarin ya bayyana sosai, zanga-zanga ta barke a kasar.
Kungiyar da ke taimaka wa mata zubar da ciki;
Duk matar da take bukatar zubar da ciki a dole ne sai dai ta je makwabciyar kasar, kamar Austria ko Jamhuriyar Czech ta yi.
Sai dai ba kowacce mace ba ce take da wannan dama, domin abu ne mai wuyar gaske ga matan da suke a kananan kauyuka na karkara, inda kowa ya san kowa, ko kuma wasu da suka dogara ga wasu da ke tallafa musu, in ji wata mata.
Matan da suke irin wannan hali sukan samu taimako ne daga wata kungiya da ake kira Abortion Without Borders.
Kungiyar ta gamayyar wasu kungiyoyi shida na Tarayyar Turai tana taimaka wa matan da ke bukatar zubar da ciki daga Ireland da Arewacin Ireland da Isle of Man da Malta da Gibraltar da Poland.
Wadda ta kafa kungiyar da ke zaune a Birtaniya Mara Clarke ta ce kungiyar ta samu karuwa sosai, ta masu bukatar a taimaka musu daga Poland duk da halin da ake ciki na annobar korona.
A cikin shekarar da ta gabata, kungiyar ta taimaka wa mata dubu 34 daga Poland samun zubar da ciki.











