Kotun Kolin Mexico ta halatta zubar da ciki

Asalin hoton, Reuters
Kotun kolin Mexico ta yanke hukuncin haramta duk wata doka da jihohi kan yi da sunan kare rai, a matsayin wadda ta saba wa kundin tsarin mulki.
Wannan ita ce nasara ta biyu a cikin kwanakin nan ga kungiyoyin mata da masu kare hakkin mata a Mexico bayan da tun a baya Kotun Kolin ta haramta ayyana zubar da ciki a matsayin laifi.
Duk da cewa ana ganin za a dauki lokaci kafin a tabbatar da wannan sabon mataki a matsayin doka a kasar, to amma masu rajin kare hakkin mata na cewa an samu sauyi sosai kan yadda ake daukar batun zubar da ciki a shekarun nan a Mexico.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan mako ya kasance gagarumi ga masu rajin kare hakkin mata musamman kan batun ciki ko haihuwa a Mexico
Bayan muhimmin hukuncin da Kotun Kolin kasar ta yi a farkon wannan mako, wanda ya ayyana zubar da ciki a matsayin abin da bai saba doka ba, a takaice ya halatta zubar da ciki.
A yanzu kuma Kotun ta yi wannan hukuncin kari a kan wancan na baya da kuma ta zartar da cewa dokokin da jihohin kasar ta Mexico kan yi da sunan kare rai tun daga daukar ciki sun saba wa kundin tsarin mulki.
Bayan da aka dage haramcin zubar da ciki a Mexico City shekaru da dama da suka gabata, jihohin kasar da yawa sun rika yin dokoki cikin hanzari a kokarinsu na sanya matakan hana zubar da ciki a dokokinsu.
Sai dai bayan da aka shigar da shari'a inda aka bukaci Kotun Kolin kasar ta yi hukunci a kan irin wannan doka ta hana zubar da ciki a jihar Sinaloa, sai alkalan Kotun suka bayar da umarnin cewa daga yanzu duk masu shari'a a kasar su rika amfani da ka'idojin da Kotun Kolin da suka kare 'yancin mata da kuma masu ciki wajen yanke hukunci.
Wannann hukunci ya kasance a matsayin mataki na gaba na karfafa damar zubar da ciki, bayan da Kotun daman ta yanke hukuncin cewa jihar Coahuila ta saba wa tsartin mulki da take hukunta mata da abokan mu'amullarsu da ma'aikatan lafiya kan saboda sun zubar da ciki.

Asalin hoton, Getty Images
Masu kare 'yancin mata a Mexico na murnar wannan hukunci, amma kuma sun kwana da sanin cewa za a dauki lokaci kafin a kai ga samun damar zubar da ciki na doka kuma maras hadari a fadin kasar.
Har yanzu ga alama akwai wasu jiga-jigai da kuma manyan masu fadi-a-ji a Cocin kasar da wannan sauyin hukunci bai yi wa dadi ba, kuma suke ki.
Sai dai da yawa 'yan kasar na da kwarin guiwa cewa hatta a kasar wadda ke zaman ta biyu a Latin Amurka mafi yawan mabiya darikar Katolika, hukuncin Kotun Kolin a fayyace yake da jihohi ba su da zabi, dole su bi.
Hukuncin ya saba sosai tamkar kishiya ga sauyin da aka yi a kan dokokin zubar da ciki, a makwabciyar Mexicon ta baryar iyakar arewa, wato jihar Texas ta Amurka, wadda a kwanakin nan ta yi dokar da ta haramta zubar da cikin da ya kai sati kusan shida.
Ko da yake Gwamnatin Shugaba Biden, wadda hukuncin bai yi dadi ba ta shigar da kara a kai.











