Yadda ake safarar mata masu ciki a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
'Yan sanda a Lagos da ke Najeriya, sun ce sun samu kubutar da mata masu juna biyun ne, bayan wani samame da suka kai kan wasu gidajen da ke wasu wurare hudu a jihar.
Kakakin 'yan sanda, Bala Elkana, ya ce shekarun matan sun kama daga 15 zuwa 28, haka kuma sun samu kubutar da wasu yara hudu.
Wata sanarwa da ta fito daga 'yan sandan ta ce, mafiya yawan matan an sato su ne da niyyar a yi musu ciki kuma a sayar da jariransu daga bisani.
An kama wasu mata biyu da ake zargi da hannu a wannan lamari, ko da yake babban wanda ake zargi ya arce, bayan ya samu labarin cewa 'yan sanda za su kai samamen.
Jami'an 'yan sanda sun ce ana sayar da jarirai maza kan sama da naira dubu 506 ($ 1,400) yayin da mata kuma kan sama da naira dubu 300 ($830).
Sai dai a cewar wata jaridar kasar, Guardian newspaper, wasu daga cikin matan da suka yarda a sayar da jariran nasu sun yi zargin cewa ba a ba su kudaden da aka yi musu alkawari ba.






