“Mun sha bakar wuya a makarantar kangararru ta Kaduna”

Isa Ibrahim
Bayanan hoto, Isa Ibrahim ya ce ya yi yunkurin guduwa kwana daya kafin 'yan sanda su gano gidan
    • Marubuci, Ishaq Khalid
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Kaduna

Daya daga cikin mutanen da aka ceto daga wata cibiya da hukumomi suka kira "wurin azabtarwsa" birnin Kaduna na Najeriya ya bayyana cewa rayuwa a gidan tamkar "zama a cikin wuta" ne.

"Idan kana yin sallah za su yi maka duka. In kana karatu ma su yi maka duka. Ko bacci kake idan za su tashe ka sai su yi maka bulala," in ji Isa Ibrahim, mai shekera 29, a hirarsa da BBC.

Tun farko dai rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar ta Kaduna ta ce mutanen da aka kubutar sun kai 300 zuwa 500 amma yanzu mutane 190 aka mika wa Ma'aikatar Ayyukan kyautata Rayuwar bil Adama da Zamantakewa ta jihar.

Wasu daga cikin su sun tsere yayin samamen, kamar yadda Hajiya Hafsat Baba, kwamishinar ma'aikatar, ta shaida wa BBC.

'Yan sanda sun ce wurin bautar da bil adama ne, inda akasarin mutanen ciki suke daure da sarka ko kuma mari.

Jami'ai sun ce wasu daga cikin su ma an ci zarafinsu.

Mutum bakwai aka kama wadanda suka hada da wasu malamai, gwamnati kuma ta ce za ta yi bincike game da sauran cibiyoyi irin wannan.

Wasu da aka daure da sarka kenan bayan an kubutar da su a jihar kadunan Najeriya, 26 ga Satumba, 2019.

Asalin hoton, Reuters TV

Bayanan hoto, Wasu daga cikin "daliban" makarantar yara ne 'yan shekara biyar

Halin da Isa Ibrahim ya shiga

Isa ya ce 'yan uwansa ne suka kai shi cibiyar mako biyu da suka gabata domin, a cewarsu, ya samu nutsuwa. Ya ce ya yi yunkurin guduwa daga cibiyar kwana daya kafin 'yan sanda su kai samame.

Ya bayyana yadda aka rika daure shi da mari sannan kuma a yi masa abin da ake kira "tarkila" watau daure hannayensa ta baya a rataye shi a jikin rufin daki yana reto kansa ta kasa.

Isa Ibrahim yana nuna tabon kuna a jikinsa
Bayanan hoto, Isa Ibrahim ya ce an sha daure shi a jikin rufin sili

"Akwai tabo iri-iri a jikina, kusan duk sassan jikina ma tabo ne," in ji shi.

Ya ce ya sha fama da yunwa kuma gayar shinkafa kawai ake ba shi. Mutanen da ke cikin gidan nan sai da "muka rasa kuzari baki dayanmu".

Akwai kananan yara 'yan shekara biyar da aka kubutar daga makarantar, wadda aka yi imanin cewa ta dade tana aiki.

Baki dayan manya da yaran da ke cikinta Najeriya ne ban da wasu guda biyu da aka ce 'yan kasar Burkina Faso ne.

Presentational grey line
Hoton cikin ginin makarantar Daru Imam Ahmad Bun Hambal a ranar 27 ga watan Satumban 2019

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wannan shi ne cikin ginin makarantar Daru Imam Ahmad Bun Hambal

Bayanai dai na nuni da cewa cibiyar mai suna Daru Imam Ahmad Bun Hambal ta karatun Islamiyya ce da gyara tarbiyyar kangararru, sai dai hukumomi sun ce munanan abubuwa na faruwa a cikin ta.

Yanzu haka 'yan sanda ne ke iko da ginin makarantar, wanda ke kama da gidan yari - yana zagaye da doguwar katanga kuma kewaye da wayoyi.

Kazalika, kofarsa babba ce mai kwarin gaske da kuma dakuna masu dan dama masu kananan tagogi.

Lokacin da BBC ta ziyarci ginin ta tarar da kayayyaki kamar katifu da botikai da tufafi da kuma litattafai, wadanda ke yashe.

Wasu daga cikin mutanen unguwar Rigasa, inda cibiyar take, sun shaida wa BBC cewa sun kadu sosai da abin da 'yan sandan suka bayyana game da cibiyar.

Daliban makarantar ba sa zuwa bara kamar yadda aka saba ganin almajiran makarantun allo.

Wasu daga cikinsu sun ce sun shafe shekaru ba tare da sun fita waje ba.

Presentational grey line
Hoton cikin ginin makarantar Daru Imam Ahmad Bun Hambal a ranar 27 ga watan Satumban 2019

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Makarantar ta debi shekaru tana aikace-aikacenta

Bayan kubutar da mutanen, an kai su sansanin aljhazai na Mando da ke jihar ta Kaduna inda mutane ke zuwa domin gano 'yan uwansu da kuma karbar su.

Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa an sha hana su ganin 'yan uwan nasu a lokacin da suke cibiyar.

Wasu daga cikin iyayen sun ce da sun san haka ake azabtar da 'ya'yansu da ba za su kai su cibiyar ba.

"Wannan wani hannunka mai sanda ne," in ji Hafsat Baba. Ta kara da cewa idan har irin wadannan abubuwa na faruwa a birnin Kaduna to ina ga yankunan karkara.

"Lallai za mu yi bincike game da irin wadanna cibiyoyi. Idan har sun saba wa doka to wajibi ne a rufe su baki daya."

Ta ci gaba da cewa: "Idan har muka gano wasu ciboyi da ke azabtar da yara ko cin zarafin mutane kamar haka za a gurfanar da su a gaban kotu."

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da wannan lamari, sannan ya shawarci malamai addini da sarakunan gargajiya da su "fallasa duk wani cin zarafi da ke gudana a cikin al'umma".