Buhari ya yi tir da cin zarafin yara a 'gidan azabtarwa' na Kaduna

FACEBOOK/BUHARI SALLAU

Asalin hoton, FACEBOOK/BUHARI SALLAU

Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tir da rahoton da aka fitar kan wani ''gidan azabtarwa'' a jihar Kaduna inda 'yan sanda suka ceto kusan mutum 500.

Kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban wato Malam Garba Shehu ya fitar, shugaban ya yi tir da duk wani nau'i irin na take hakkin bil' adama ga yara ko manya.

Bayan shugaban ya jinjina wa rundunar 'yan sandan kasar da irin jajircewarta na gano irin wannan ''mummunan wuri,'' ya kuma yi kira da a yi kokarin kiyaye kananan yara daga duk wani mugun abu da ke cikin al'umma.

Shugaban ya kuma yi kira ga malamai da sarakunan gargajiya da su bai wa gwamnati hadin kai don kare sake afkuwar abin da ya kira ''al'adar azabtar da yara da sunan ladabtar da su.''

A makon nan ne dai 'yan sandan kasar suka ceto kusan mutum 500 a wani gini da ake tsare da su a birnin Kaduna.

Baki daya mutanen dai maza ne, manya da yara, wasu an daure su da mari ko sarka.

Makarantar dai wacce an kai yawancin yaran ne daga jihohin makofta da nufin ladabtar da su da koya musu karatun addini, amma kuma sai ya kasance ana azabtar da su, da cin zarafinsu ta hanyar lalata da sauran nau'in mugunta.

Wasu daga cikin yaran 'yan shekara bawaki zuwa 10 ne, ana kuma tsare da su ba shiga, ba fita daga makarantar na wasu shekaru.

Sai dai malaman addinin musulunci a Nigeria sun yi watsi da rahotannin da ke cewa makarantar ta islamiyya ce.

Me wasu 'yan Najeriya ke cewa dangane da wannan batu?

Tun bayan afkuwar wannan lamari, jama'a da dama na bayyana ra'ayoyinsu musamman a shafukan sada zumunta dangane da wannan batu inda da dama suke nuna rashin jin dadinsu da afkuwar wannan lamari.

Kauce wa Facebook, 1

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook, 1

Babawo Mato Mai'adua a shafin Facebook ya gargadi iyaye a kan kai yaransu irin wadannan makarantu domin gyaran tarbiyya.

Kauce wa Facebook, 2

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook, 2

A ra'ayin Adam Omajudo ya nuna cewa bai kamata a hana irin wadannan makarantu ba domin kuwa suna shiryar da yara.

Kauce wa Facebook, 3

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook, 3

Sai kuma Usman Mohd Zaria yabo ya yi ga 'yan sandan Najeriya kan irin kokarin da suka yi wajen gano irin wannan makaranta.