'Hana 'yan mata masu ciki zuwa makaranta a Saliyo ba daidai ba ne'

Asalin hoton, Getty Images
Wata kotun kasashen Yammacin Afirka ECOWAS ta yanke hukuncin cewa matakin da gwamnatin Saliyo ta dauka na haramta wa 'yan mata masu ciki zuwa makaranta ya kauce wa ka'ida kuma ya kamata a gaggauta soke shi.
Matakin kotun ya samu goyon bayan kungiyoyin kare hakkin dan Adam irin su Amnesty International.
Kunigyar Amnesty ta ce hukuncin kotun zai zama darasi ga sauran kasashe masu irin wannan haramcin kamar Tanzaniya da Equitorial Guinea.
Kotun ta ce haramta wa 'yan matan zuwa makaranta nuna wariya ne kuma ya kauce wa dokokin kare hakkin bil Adama.
Gwamnatin Saliyo ta kakaba haramcin ne shekara hudu da suka gabata, lokacin da aka samu karuwar 'yan mata masu samun ciki a waje saboda illar da cutar Ebola ta yi a kasar.
Illar da cutar ta yi a kasar ta daidaita iyalai, tare da jefa 'yan mata da yawa cikin maraici da saukin fadawa cikin hadari.
Gwamnatin ta ce dalilin haramcin shi ne saboda 'yan matan ba za su samu kuzarin zuwa makaranta da juna biyu ba, kuma za su iya gurbata tarbiyyar kawayensu.
An bude makarantu na musamman saboda 'yan mata masu ciki amma kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce makarantun ba su da inganci kamar saura, kuma suna iya dakile cigaban 'yan matan.











