Intanet na 'shafar' walwalar 'yan mata

Amfani da waya na alaka da walwalar kwakwalwar yara a cewar binciken
Bayanan hoto, Amfani da waya na da alaka da walwalar kwakwalwar yara a cewar binciken

Samun barci da zama tare da abokai ya fi shafar walwalar 'yan mata a kan amfani da kafafen sada zumunta da muhawara n intanet a cewar wani rahoto.

Binciken rahoton na kasa wanda aka gudanar ya yi nazari ne a kan farin cikin matasa.

Amfani da kafafen sada zumunta da muhawara ba ya shafar walwalar 'yan mata sai dai suna rasa barci ko kuma ana musguna masu a kan kafafen.

Cin zali na shafar walwalarsu fiye da shafukan zumunta muhawara.

Duk da muhawarar da ake ci gaba da yi a kan yadda shafukan sada zumunta da muhawara suke shafar matasan, rahoton ya nuna babu wata alaka tsakanin damuwa da yanayin lafiyar kwakwalwarsu.

'Abota'

Samun lokaci tare da abokai da samun isashen barci su ne "hanyoyin kariyar lafiyar kwakwalwar dukkanin matasa" a cewar rahoton na ma'aikatar ilimi.

Cin zali shi ne babban abin da ke shafar lafiyar kwakwalwar 'yan mata kanana, amma bai da tasiri sosai ga manyan mata.

Rahoton ya kare da cewa "amfani da kafafen sada zumunta da muhawara shi ne mafi karanci cikin halayen da muka duba, samun isashen barci da kuma samun lokaci tare da abokai ya fi illa sau uku".

"Idan ana cin zalin mutum, ko da a kafafen intanent ne ya fi illa ga lafiyar fiye da sau takwas."

'Matsi'

Sakataren ilimi Gavin Williamson ya ce "Matsin da matasa suke fuskanta a yau a makaranta ko a wajenta, mafiya yawa sun sha bamban ne daga irin na iyayensu da kakanninsu. Ya kamata mu saurare su kuma mu yi aiki da abin da suka ce."

Ya kara da cewa: "Abin sha'awa ne cewa mafi yawan yara suna zama cikin farin ciki ne, amma hakki ya rataya a wuyanmu da mu kara kaimi domin faranta wa wadanda ba su yi."

"Mun bai wa malaman makaranta dama su hukunta halaye marassa kyau irin su cin zali domin makarantu su samu zama tsabtatattun wuraren da yara za su habaka. Rahoton yau ya taimaka wurin karin haske ga inda ya kamata a mayar da hankali."

A watan Oktobar 2018 ne Firai Minista Theresa May ta sha alwashin buga rahoton bincike na kasar domin tabbatar da hujjojin a kan walwalar kananan yara, domin kuma samar da mafita a bisa hujjar da za ta shiryar zuwa ga daukar mataki.