'Yan kasar Afghanistan na fuskantar 'bala'i' a yayin da hunturu yake matsowa

An rabawa matan Afghanistan abinci lokacin azumin Ramdan a Jalalabad

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Miliyoyin 'yan Afghanistan sun dogara kaco kan kan abincin da hukumar samar da abinci ta duniya ke bayar wa
    • Marubuci, Daga John Simpson
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Bamiyan, central Afghanistan

Wannan kasa ce da ta soma fuskantar matsalar yunwa .

Yanayin yana sauyawa daga yanayin da ake shiga bayan damina zuwa na hunturu.Yankuna da dama sun bayar da rahoton fari , wanda yana cikin abubuwan da suka janyo bala'in.

A Maidan Wardak, mai nisan kilomita 50 da Kabul, wasu maza sun taru da fatan samun garin fulawa daga wata cibiyar raba kayan masarufi .

Hukumar samar da abinci ta duniya ce ta samar da garin fulawar.

Mayakan Taliban sun taimaka wajen ganin an yi rabon ba tare da wata matsala ba, sai dai mutanen da aka ce ba su cancanci a ba su a hannu ba sun fusata kuma sun bayyana fargaba.

"An kusa fara sanyi a wannan wuri,'' in ji wani dattijo. "Ban san yadda zan yi rayuwa ba idan ban iya samun burodi ba ".

Hukumar samar da abinci ta duniya watau WFP na fuskatar matsala a kan yadda za ta kara yawan kaya agaji ga Afghanistan domin taimaka wa mutum miliyan 22.

Idan yanayi ya yi muni kamar yadda masana suka yi hasashe a wannan sanyi, abin da hakan ke nufi shi ne mutane da yawa za su fuskanci barazanar matsananciyar yunwa .

Na yi magana da babban diraktan WFP, David Beasely, lokacin da ya kai ziyara Kabul a ranar Lahadi.

Binciken da ya yi game da lamarin yana da ban tsoro.

" Abin ya yi muni fiye da yadda ake tunani," in ji Mista Beasley. " A gaskiya, yanzu muna fuskantar matsalar jin kai da ba a taba ganin irinta ba a duniya.

"Kashi 95 cikin dari na alummar kasar ba su da isashen abinci kuma a yanzu mutum miliyan 23 na dab da fadawa cikin yunwa," in ji shi . " Za a shiga cikin halin ka-ka-ni -ka-yi a cikin watanni shida masu zuwa .

Kafin Taliban ta kwace iko a Afghanistan a watan Agustan da ya gabata, an samu kwarin gwiwar cewa gwamnatin shugaba Ashraf Ghani za ta iya tinkarar barazanar da ake fama da ita a lokacin sanyi, idan aka yi la'akari da taimakon kasashen yamma. Sai dai wannan taimakon ya fuskanci koma baya lokacin da gwamnatin Mista Ghani ta wargaje.

Kasashen yamma sun dakatar da tallafin da suke bai wa kasar, saboda ba sa son a ga sun taimka wa gwamnatin da ta hana 'ya 'ya mata samun ilimi wadda kuma ta ke goyon bayan dawo da cikakken hukuncin shari'ar musuluci.

Amma shin ko waɗannan ƙasashe za su bar miliyoyin mutane da ba su aikata laifi ba su fuskanci matsananciyar yunwa?

Mista Beasley ya kalubalanci gwamnatoci da attajiran kasashen da su tashi tsaye wajen bada da agajin da ake bukata cikin gaggawa.

Wani sojan Taliban na gadi yayin da mata sun yi layi a shirin raba abinci na hukumar samar da abinci ta duniya a Kabul

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani soja Taliban ya tsaya yayin da mata sun yi layin abinci a Kabul

A karkashin gwamnatin da ta gabata Fatema ta sami damar samun kayan abinci da suka hada da fulawa da kuma man girki, , amma an dakatar da bayar da wadannan abubuwa bayan da Taliban suka karbe iko.

Fateema ta kasance tana samun kuɗi kaɗan tana yayyafa ƙasa ga wani manomi da ke kusa. Sai dai yanzu, fari da ke addabar wannan yanki yana nufin cewa amfanin gona kaɗan ne suka tsira, kuma babu aiki a gare ta.

"Ina jin tsoro," in ji ta. "Ba ni da abin da zan ba yaran. Nan ba da jimawa ba zan fita bara."

Wasu iyaye sun sayar da 'ya'yansu mata ga maza domin su auresu . Fateema ta ki yin hakan. Sai dai idan ba a dawo da tsarin bada abinci ba, ita da 'ya'yanta za su fuskanci tsananin yunwa.

Yanzu da dusar ƙanƙara ta fara zuba a saman tsaunin da ke kusa nan bayar da jimawa ba za a fara jin sanyi kuma ɗimbin mutane kamar Fateema da iyalinsu za su kasance cikin bala'i.