Harin bam ya hallaka mutum 25 a Afghanistan

Sama da mutum 25 ne suka mutu wasu akalla 16 suka ji mummunan rauni, a harin wuta da tashin bam a asibitin sojoji da ke Kabul babban birnin Afghanistan.
Jami'ai sun ce maharan sun far wa asibitin Sardar Daud Khan, mai gado 400, inda suka fara da tada bama-bamai biyu a wajen asibitin, kafin daga bisani suka shiga cikinsa tare da bude wuta.
Tuni wata kungiya mai alaka da IS ta dauki alhakin kai harin. Hotuna da bidiyo da aka yada a shafukan das zumunta daga Kabul, sun nuna yadda hayaki ya turnuke sararin samaniya tare da karar harbin bindiga.
Wani likita ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, ya gudu wani wuri domin fakewa inda anan ma yak e ta jin ana luguden wuta.
Dakta Sayed Ahad ya ce daya daga cikin tashin bam din na kunar bakin wake ne.
"A matsayi na na dan Afghanistan, na gaji da wannan yakin, na gaji da harin kunar bakin wake da dasa bama-bamai. Har tsahon wane lokaci za a dauka ana sanya rayuwarmu cikin ukuba da bala'i?"
Mai Magana da yawun kungiyar Taliban Bilal Karimi, ya shaidawa BBC cewa mayakan kungiyar IS sun shiga harabar asibitin, tare da dasa bam na farko daga a daidai kofar shiga.
Mista Karimi ya kara da cewa su ma mayakan Taliban sun maida martini t hanyar budewa daya daga cikin maharani wuta da cafke guda a raye.
Shi ma babban mai Magana da yawun Taliban Zabihullah Mujahid, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa mayakan Taliban na musamman da jirgi mai saukar ungulu ya sauke mayaka inda suka hana maharani shiga cikin asibitin.
Ganau sun shaidawa Reuters cewa sun ga jirage masu saukar ungulu biyu a lokacin da aka aki harin. Shi ma wakilin Reuters y ace wannan shi ne karon farko da mayakan Taliban sukai amfani da jirgi mai saukar ungulu da suka kwace a baya-bayan daga hannun gwamnatin da kasashen yammacin duniya ke marawa baya.
Wannan hari dai shi ne mafi muni da aka kai Afghanistan, tun bayan karbe iko da kasar da Taliban ta yi a watan Agusta da ya wuce, bayan janyewar dakarun Amurka daga kasar.
Asibitin sojoji na Sardar Daud Khan ya sha fama da hare-hare irin wannan. Ko a shekarar 2017 sama da mutum 30 suka mutu wasu 50 suka ji rauni, lokacin da maharani da sukai badda kama cikin kayan likitoci suka far wa asibitin tare da bude wuta, shi ma wannan harin kungiyar IS ce ta dauki alhakin kai shi.











