Jaririyar da iyayenta suka sayar da ita dala 500 saboda talauci

Bayanan bidiyo, Iyayen da suka sayar da 'yarsu $500 domin sayen abinci a Afghanistan

Latsa hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon

Afghanistan tana fuskantar babban bala'in yunwa da neman agaji a duniya, inda lamura suka sake tabarbarewa tun watan Agusta lokacin da Taliban ta kwace iko.

Manyan kasashen duniya sun dakatar da kudin da suke bai wa kasar wadanda suke tallafa wa tattalin arzikinta da ke tangal-tangal yayin da ake tattaunawa kan yadda za a yi hulda da gwamnatin Taliban.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi mai ƙwari inda ta ce miliyoyin mutane za su mutu idan ba a kai musu agajin gaggawa nan ba da jimawa ba.

A wannan bidiyon, wakiliyar BBC Yogita Limaye ta je Herat da ke yammacin kasar, inda ta shaida yadda lamura suka tabarbare.

Mai tsara shirin: Imogen Anderson

Wanda ya dauki shirin da tace shi: Sanjay Ganguly