Sudan: An kashe masu zanga-zanga uku da ke adawa da juyin mulki

Asalin hoton, AFP
Dubban 'yan Sudan ne suka sake cika titunan kasar a wata sabuwar zanga-zangar kin amincewa da juyin mulkin da sojoji suka yi tare da bukatar a maida mulki hannun farar hula.
Masu zanga-zanga a babban birnin kasar Khartoum da sauran birane, sun bukaci a gaggauta maido Firai Minista Abdullah Hamdok kan mukaminsa.
Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaro sun harbe mutum uku a biranen Khartoum da Omdurman.
A makon da ya wuce ne jagoran juyin mulkin Janaral Abdel Fattah Burhan, ya wargaza gwamnatin farar hula tare da cafke shugabannin siyasa.
Janaral din da ya ayyana dokar ta-baci, ya ce, ''na dauki matakin ne domin kauce wa fadawar kasar cikin yakin basasa tare da dakatar da rikicin siyasa.''
Juyin mulkin da sojojin Sudan suka yi ya janyo alla-wadai daga sassa daban-daban na duniya.
A ranar Asabar masu zanga-zanga a Khartoum suka cika tituna dauke da tutar kasar tare da rera waken ''Ba mu amince da mulkin soja ba.''
Kungiyar likitoci a Sudan ta bayyana cewa an kashe masu zanga-zanga uku a birnin Omdurman.
Sai dai ma'aikatar cikin gida ta musanta cewa jami'an tsaro sun yi amfani da harsashi kan masu boren, tare da zargin masu zanga-zanga da kai wa 'yan sanda hari.
Daga yin juyin mulkin kawo yanzu an kashe masu zanga-zanga 10, a taho-mu-gama tsakaninsu da jami'an tsaro.

Asalin hoton, AFP
Hukumomin Sudan sun katse layukan wayar salula da na intanet, tare da sanya dokar takaita zirga-zirga.
Kafin juyin mulkin da aka yi a ranar Litinin din makon jiya, gwamnatin farar hula da sojoji na fama da rikici tsakaninsu, kan rarraba mukamai kamar yadda suka yi alkawari lokacin da aka hambarar da mulkin shugaba Omar al-Bashir a shekarar 2019, wanda ya jagoranci Sudan sama da shekara 30.
Sun cimma matsayar da ake fatan za ta mayar da kasar kan turbar dimukradiyya, amma sai lamarin ya fuskanci turjiya sakamakon yunkurin juyin mulki da aka yi ta yi da bai yi nasara ba, na baya-bayan nan shi ne wanda ya faru a watan da ya gabata.
A bangare guda kuma Janaral Burhan wanda shi ke jagorantar kwamitin mulkin hadaka ya nanata cewa har yanzu Sudan na kan bakanta na mika mulki ga farar hulha da zai tabbatar da kasar kan turbar Dimukradiyya, inda za a gudanar da zabe a watan Yulin shekarar 2023.











