An dakile yunkurin juyin mulki a Sudan

Asalin hoton, AFP
Kafar yada labaran talabijin ta Sudan ta tabbatar da yunkurin juyin mulki a kasar.
Sai dai ba ta bayyana ko su waye suka yi yunkurin kifar da gwamnatin ba.
Rahotanni daga babban birnin kasar wato Khartoum da kuma Omdurman na cewa an baza sojoji kan titi an kuma rufe gadojin da ke mahadar kogin Nilu.
Jaridar AFP ta ambato majiyar gwamnati na cewa makitsan juyin mulkin sun yi kokarin kwace ginin gidan talabijin na kasar.
Kazalika hotunan da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna tankokin yaki na yawo a kan manyan tituna.
Hukumomin Sudan sun ce suna kan daukar matakan daidaituwar al'amura a kasar.
Kamar yadda jaridar Reuters ta ruwaito kakakin gwamnati Mohamed Al Faki na fada, ba da jimawa ba za a fara binciken wadanda ake zargi da kitsa juyin mulkin.
Shekaru biyu da suka wuce ne a ka kifar da gwamnatin tsohon Shugaba Omar Albashir, sannan a ka kafa gwamnatin riko da ta kunshi sojoji da fararen hula.
An samar da gwamnatin hadaka ta sojoji da wakilan fararen hula da kungiyoyin masu zanga-zanga bisa yarjejeniyar kara-karba bayan kifar da Shugaba Bashir a shekarar 2019.
Sashen da ke sa ido na BBC ya ruwaito cewa an sha kokarin yin juyin mulki a Sudan tun faruwar wancan lamarin.
Gwamnatin Sudan ta ce komai ya lafa a yanzu.
Bidiyon da aka yada a ranar TAlata da safe ya nuna motocin tankokin yaki a kan tituna, amma kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa a yanzu babu cunkoson motoci a yankin tsakiyar Khartoum.
Kamfanin dillancin labarai na Reurters ya ce mai magana da yawun sojin kasar Mohamed Al Faki Suleiman ya ce nan ba da jimawa ba za a fara tuhumar wadanda ake zargi da yunkurin juyin mulkin.











