Ananya Pandey: Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta India ta yi sammacinta

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta India ta yi wa daya daga cikin matasan jarumai mata na India wato Ananya Pandey, tambayoyi makonni bayan hukumar ta kama dan gidan jarumi Shahrukh Khan bisa zargin ta'ammali da kwayoyi.
Hukumar ta NCB, ta ce ta yi wa Ananya Pandey tambayoyi ne ba wai a kan abin da ke da alaka da dan Shahrukh Khan Aryan Khan ba ne.
Kazalika hukumar bata bayyana dalilin da ya sa ta gayyaci Ananya zuwa ofishinta da ke Mumbai ba.
Ananya Pandey, wadda 'ya ce ga jarumi Chunky Pandey, ba ta bayyana dalilin da ya sa aka kira ta zuwa ofishin hukumar yaki da miyagun kwayoyin ba.
Ba Ananya ce jarumar da hukumar ta kira ofishinta domin yi mata tambayoyi ba a baya bayan nan, ko a makonnin da suka wuce hukumar ta kama tare da tsare Aryan Khan, dan Shahrukh Khan, bisa zarginsa da ta'ammali da kwayoyi matakin da ya janyo suka daga mutane da dama ciki har da jarumai a kasar.
An dai kama Aryan Khan ne a ranar 2 ga watan Oktobar, 2021, a cikin jirgin ruwa wanda ke kan hanyarsa daga Mumbai zuwa Goa.
An kama shi saboda zarginsa da mallaka da sha da kuma sayar da kwaya, abin da lauyansa ya ce ba bu wata shaida da ta nuna cewa Aryan ya sha kwayam haka kuma ba a same shi da kwaya a tare da shi ba.
Duk kokarin da lauyoyin Aryan suka yi na bayar da belinsa ya ci tura kusan sau biyu.
Sammacin Ananya da kama Aryan Khan, sun zamo labaran da suka mamaye kafofin yada labarai na kasar ta India.
Wasu na ganin kamar bita da kulli ake yi wa Shahrukh Khan, shi ya sa aka kama dan nasa a kan zargin ta'ammali da kwayoyi.
Tun a shekarar da ta wuce da 2020, hukumar ke yawan sammacin jarumai ko kuma masu gabatar da shirye-shirye a Talbijin din kasar in da take yi musu tambayoyi ko kuma gudanar da bincike a kansu.Daga cikin wadanda hukumar ta yi wa tambayoyi a 2020, akwai jaruma Deepika Padukonem da Rhea Chakraborty.
Hukumar dai na yawan zargin jaruman da ta'ammali da kwayoyi abin da ke janyo wasu na kashe kansu, kamar misalin jarumi Sushant Rajput, da aka tsinci gwarsa a gidansa bayan ya rataye kansa a 2020.











