Bollywood: Abin da ya kashe auren Aamir Khan da matarsa Kiran Rao na shekara 15

Asalin hoton, Reuters
Fitaccen jarumin fina-finan Indiya, Bollywood Aamir Khan da Furodusa kuma darakta Kiran Rao sun sanar da mutuwar aurensu bayan shekara 15 da kasancewa a matsayin miji da mata.
Cikin wata sanarwa, sun ce za su ci gaba da gudanar da ayyuka da kuma tarbiyyantar da dansu tare.
Kham mai shekara 56 da Rao mai shekara 47 sun fara haɗuwa a 2001 sannan shekara huɗu bayan nan, suka yi aure.
Sun ce suna son buɗe wani sabon babi a rayuwarsu - ba a matsayin mata da miji ba sai dai a matsayin iyaye na gari ga ɗansu.
Sun ƙara da cewa alaƙarsu ta bunƙasa cikin aminci da girmama juna da kuma ƙauna".
Cikin shekarun da ya shafe a harkar fina-finai, Khan ya gina sunansa a matsayin ɗaya daga cikin shahararrun ƴan wasan Bollywood inda yake da tarin magoya baya a Indiya da kuma sauran ƙasashen duniya musamman China.
A shekarar 2015, Khan wanda musulmi ne ya ja hankalin jaridu saboda kalaman da ya yi cewa akwai rashin haƙuri a Indiya.
Kalaman nasa sun janyo masa suka daga jam'iyyar BJP mai mulki amma kuma Khan ya ce shi ko matarsa wadda Hindu ce ba su da niyyar barin ƙasar.
Ya bayyana cewa bai ji daɗin yadda mutane suka kira sa "mai adawa da ƙasa" da yi masa ihu kawai don ya fadi ra'ayinsa.
A baya dai, Khan ya auri Reena Dutta da suka haifi yara biyu.











