Zainab Booth: 'Yar wasan kwaikwayo kuma mahaifiyar Maryam Booth ta rasu

Asalin hoton, Maryam Booth
'Yar wasan fina-finan Kannywood, Hajiya Zainab Booth, wadda ke jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta rasu bayan fama da rashin lafiya.
Ta rasu ne a birnin Kano da daren Alhamis, a cewar danta Umar Booth, a tattaunawarsa da BBC.
Ta rasu tana da shekaru 61 a duniya.
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, hakika Allah cikin ikonsa ya yi wa mahaifiyarmu Hajiya Zainab Booth rasuwa bayan fama da rashin lafiya, ta rasu a daren Alhamis da misalin karshe 9 na dare, za a yi jana'izarta a yau Juma'a idan Allah ya kai mu.
Ta rasu ta bar 'ya'ya hudu, maza biyu da mata biyu, wato Ni Umar, sai Amude da Maryam da kuma Sadiya, sai jikoki guda biyu," in ji Umar.
Umar ya kara da cewa za a tuna da Hajiya Zainab Booth da son zumunci da yawan yin addu'a, sannan ita din uwa ce ga kowa don haka ne ma duk inda ta shiga za ka ji ana kiranta Mama, Mama.
A kwanakin baya ne dai marigayiyar ta yi fama da rashin lafiya lamarin da ya kai har an yi mata aiki a kwakwalwa, kamar yadda 'yarta Maryam Booth ta dinga wallafa hotunan a shafukan sada zumunta.
Marigayiyar ta kasance daya daga cikin taurarin Kannywood da 'ya'yanta uku suka kasance su ma taurari.
An yi jana'izarta a gidanta da ke birnin Kano da misalin karfe takwas na safiyar Juma'a.
Kannywood ta fada halin alhini
Tuni dai taurari da sauran masu ruwa da tsaki a Kannywood suka soma alhinin rasuwar Hajiya Zainab Booth.
Taurari da furodusoshi da saura masu ruwa da tsaki irin su Ali Nuhu da Falalu Dorayi da Aminu Saira sun yi addu'ar Allah ya jikanta.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Aminu Saira ya yi mata addu'a kamar haka:
"Allah ya jikan ki da Rahama Hajiya Zainab, Allah ya yafe kura-kuran ki, Allah ya sa aljannah ta zama makomar ki".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram, 1
Shi ma Ali Nuhu cewa ya yi: "Innalillahi wa inna ilahir raj'un, ALLAH ya yi wa Haj Zainab Musa Booth rasuwa, gobe za a yi jana'iza a gidan ta da ke kallon Premiere Hospital a Court Road da karfe takwas na safe (8:00am). ALLAH ya jikanta da rahama, ya sa aljanna ce makomarta, amin."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram, 2
A nata bangaren, Saratu Gidado wacce aka fi sani Daso ta mika sakon ta'aziyyarta ga iyalan marigayiyar:
"Allahu Akbar. Allah yayiwa Abokiyar Sana'ar mu ta FILM rasuwa wato Zainab Booth. Yau Alhamis 01/07/2021. Muna mika sakon Ta'aziyar mu ga Iyalinta. Allah ya yafe mata kurakurenta. @officialmaryambooth".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram, 3