Za a yi wa yaran Afirka riga-kafin cutar Maleriya

Jami'ar lafiya na yi wa jariri allurar rigakafi

Za a yi wa yara kanana allurar riga-kafin cutar maleriya a duk fadin nahiyar Afirka, a wani abin tarihi na yaki da wannan mummunar cuta mai kisa.

Maleriya dai ta kasance wata babbar matsala da ke kashe jarirai da yara ƙanana.

Samun riga-kafin cutar bayan daukar karni guda ana fadi tashin nema, riga-kafin na daga cikin magungunan da aka amince da ingancinsu shekaru shida da suka gabata.

Yanzu bayan wani gwajin allurar rigakafin a kasashen Ghana da Kenya da kuma Malawi, Hukumar Lafiya ta Duniya, ta ce za a gudanar da shirin rigakafin a illahirin nahiyar Afirka, da sauran wuraren da ake da matsalar zazzabin cizon sauro.

Shugaban hukumar Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce lokaci ne mai cike da tarihi.

"Hakika samun rigakafin cutar maleriya ga kananan yara da aka dade ana jira, abin alfahari ne da ci gaba ga fannin kimiyya, da fannin kiwon lafiyar yara da shirin shawo kan cutar, wannan zai kubutar da dubban yara a kowacce shekara daga kamuwa da maleriya," in ji Ghebreyesus.

Cuta mai kisan kai

Cutar maleriya, cuta ce da ke kassara dan adam da lalata jini, ana kuma daukar ta ne ta hanyar cizon sauron da ke dauke da ita.

Amfani da maganin cutar da gidan sauro mai dauke da sinadarin kashe nau'in sauron da ke yada ta sun taimaka matuka wajen rage cutar.

Nahiyar Afirka shi ne yankin da cutar ta maleriya tafi yi wa illa musamman yara.

Mutum 260,000 maleriya ta yi wa ajali a shekarar 2019 kadai.

An dauki shekara da shekaru wajen gwaje-gwajen magunguna da neman allurar riga-kafin da ta dace da cutar, amma ba a yi nasara ba sai dai an samu maganin da ya ke saukakawa wanda ya kamu da cutar shan wuya.