Hukumar Lafiya ta Duniya: Yawan masu hawan jini a duniya ya karu

Asalin hoton, EPA
Wani sabon rahoto da aka fitar ya nuna cewa yawan mutanen da ke fama da matsalar hawan jini a duniya ya ninka biyu a shekara talatin da ta gabata.
Rahoton wanda Hukumar Lafiya ta Duniya tare da Imperial College ta London suka hada, shi ne bincike mafi girma irinsa da aka taba gudanarwa, ya kuma nuna cewa kusan rabin yawan mutanen da ke da larurar hawan jinin bas u ma san suna da ita ba.
Larurar hawan jini babbar matsala ce ga cutar zuciya da kuma ta shanyewar jiki, kuma tana daya daga cikin manyan abubuwan da ke janyo mutuwa da cutuka a duniya.
Matsala ce da ake ganowa cikin sauki, kuma ana maganinta, to amma abin takaicin shi ne akwai tarin mutane har miliyan 580 da ba a ma gano suna dauke da larurar ba, saboda haka ke nan sun rasa damar yi musu maganin da ake ganin zai iya ceto rayuwarsu.

Asalin hoton, SPL
An gudanar da nazarin ne a kan sama da mutane miliyan dari daya (100) a kasashe dari da tamanin da hudu (184).
Ko da yake yawan mutanen da ke da larurar ta hawan jini ya linka biyu a shekara talatin da ta gabata, amma kyakkyawan labarin shi ne cewa ainahin yawan mutanen da ke da matsalar a cikin kashi dari kusan yana nan yadda yake bai karu ba
Saboda haka karuwar ta kasance ne a dalilin habakar yawan jama'a da kuma girma ko tsufa da jama'a ke yi.
Amma kuma nauyi ko dawainiyar matsalar ta hawan jini ta sauya, ta yadda kasashen duniya da suka ci gaba, masu arziki kamar su Switzerland da Canada suke da mafiya karancin masu larurar.

Asalin hoton, Getty Images
Kasashe masu karanci da kuma matsakaicin tattalin arziki, kamar su Jamaica da Paraguay da Hungary da kuma Poland su ke da yawan masu fama da larurar.
Rahoton ya bukaci gwamnatoci da su bayar da fifiko wajen gwajin gano cutar ta hawan jini, tare da kara damar samun maganinta, domin kare yawaitar cutuka da kuma ceto rayuka.
An yi kiyasin mutane biliyan 1.13 a fadin duniya suna dauke da larurar hawan jini, yawancinsu a kasashe masu mafi karanci da kuma matsakaicin samu.

Asalin hoton, Getty Images
Hawan jini na daya daga cikin cutukan da ke haddasa mutuwar mutane da wuri a fadin duniya.
Burin da aka sanya a gaba a duniya a tsakanin shekara ta 2010 da 2015, a kan cutukan da ba a yada su, shi ne rage yawan kamuwa da cutar da kashi 25 cikin dari.
A shekara ta 2015 alkaluma sun nuna cewa a duk maza hudu, daya na dauke da matsalar, yayin da a mata biyar ake da daya. Sannan kasa da mutum daya a cikin biyar ne da ke da rashin lafiyar ke yin magani.











