WHO: 'Kasashen Afirka na baya a riga-kafin korona'

An bar kasashen Afurka a baya a yin rigakafin cutar korona

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar Lafiya ta duniya WHO, ta ce kasashen Afirka 14 ne kadai suka iya yi wa kaso 10 cikin 100 na al'ummarsu allurar riga-kafin cutar korona.

Hukumar lafiyar ta ce kasashen ba su cimma iya kason da ake so ba saboda matsalar da shirin rarraba riga-kafin ga kasashe matalauta na Covax ya fuskanta sakamakon siye rigakafin da kasashe masu arziki suka yi.

Shirin Covax dai ya kuduri aniyar raba alluran riga-kafi miliyan 274 ga kasashen Afirka kafin nan da karshen watan da muke ciki, to amma alluran fiye da miliyan biyar kadai ya iya raba wa kasashen.

Kasashen Afrikan da basu da yawan al'umma sun yi kokari sosai wajen yi wa jama'arsu allurar rigakafin cutar korona, idan aka kwatanta da Afurka ta Kudu mai yawan jama'a.

A cikin kasashen goma sha hudu, Seychelles da Mauritius da kuma Morocco ne kadai suka zarta adadin yawan wadanda ake so ayi wa riga-kafin.

An yi wa kashi 40 cikin 100 na adadin al'ummarsu cikakkiyar allurar riga-kafin Koronar.

WHO ta danganta haka da rubanya shirye-shiryensu na gudanar da allurar riga-kafin, da girman kasashen da kuma yawan al'ummarsu.

Sauran kasashen da su ma suka yi kokari wajen yin allurar riga-kafin sun hada da Tunisia da Eswatini da Cape Verde da Botswana da Comoros da Zimbabwe da Equatorial Guinea, da Afirka Ta Kudu da Lesotho da kuma Rwanda.

Yayin da Birtaniya da Amurka da kuma kasashen kungiyar tarayyar turai suka yi wa kaso 60 cikin 100 na al'umarsu allurar riga-kafin cutar koronar.

An dai bar sauran kasashen duniya da dama a baya wajen yin allurar rigakafin saboda basu karbi isassun allurarn ba daga shirin Covax na raba alluran ga kasashe matalauta.

Ana ganin cewa an samu karancin alluran ne ko kuma shirin na Covax ya gaza samar da isassun alluran ga kasashen da ya yi wa alkawari saboda kasashen da ke da arziki kan yi yarjejeniya da kamfanoni da suke samar da alluran su ba su makudan kudade domin su yi musu tasu allurar.