Riga-kafin coronavirus: Akwai wata maƙarƙashiya da ake son yi wa Musulunci kan riga-kafin korona ne?

Asalin hoton, EPA
- Marubuci, Halima Umar Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Masana kiwon lafiya sun ce yaɗa jita-jita kan riga-kafin cutar korona ba ƙaramar illa ba ce ga al'umma.
Tun bayan da aka fara yi wa mutane allurar riga-kafin kariya daga cutar korona da ta addabi duniya, mutane musamman a ƙasashe masu tasowa irin Najeriya ke yaɗa jita-jita iri-iri kan riga-kafin.
Wasu daga cikin labaran jita-jitar da ake yaɗawa sun haɗa da cewa so ake a rusa Musulunci da Musulmai a faɗin duniya.
Sai dai a wata hira da BBC ta yi da Dr Umar Jibrin Madugawa, wani likita ɗan Najeriya da ke aiki a Landan, wanda aka riga aka yi ma allurar, ya ce jahilci ne ke sa wasu yaɗa jita-jita ta ƙarya.
Tuni dai aka fara yi wa mutane riga-kafin a ƙasashe irin su Burtaniya da Jamus da Faransa da Saudiyya da Rasha da Qatar da Kuwait da sauran su da yawa.
Dr Madigawa ya yi kira ga dukkan mutanen da suke tababa kan riga-kafin da su bai wa allurar muhimmancin gaske don su yarda a yi musu ita.
"Ya fi alheri ƴan uwana baƙar fata su samu a yi musu allurar maimakon su ƙare da kamuwa da cutar Covid-19. Don ita wannan cuta ba ruwanta da yanayin fatarka ko arziƙinƙa, idan ta zo gaba ɗaya za ta yi maka.
"Don haka ina kira ga mutane su guji yarda da yaɗa jita-jita da raɗe-raɗi marasa amfani da za su cutar da mutane," in ji Dr Madigawa.

Mece ce jita-jitar da ake yaɗawa?
Tun bayan da aka sanar da cewa an amince da alluran riga-kafin da wasu manyan ƙasashen duniya suka samar aka fara baza jita-jita a ƙasashe irin Najeriya.
Ana tura saƙonni ta manhajar Whatsapp da Facebook inda ake gargaɗin mutane da cewa su guji yin allurar riga-kafin ko da ta shigo Najeriya "domin kuwa hanya ce da ake son bi a kashe mutane," kamar yadda wasu saƙonnin ke cewa.
A ɗaya daga cikin saƙonnin da BBC Hausa ta gani yana cewa:
"Bill Gate Mai kudin duniya ya kawo tayin wannan allurar riga kafi ta hannun shugaban majalisar wakilai na tarayayyar Najeriya Hon. Gbajabiamila da sauran 'yan majalisarsa akan kudurin doka da yake so ya samar na tilasta wa dukkan 'yan Nigeria karbar allurar rigakafin cuta mai yaduwa wanda Bill Gate ya dauki nauyi.
Bayanin ya ci gaba da cewa: "Wanda duk wanda aka saka masa wannan allurar ba zai wuce wata biyar mai kyau yana rayuwa ba, manufarsu ita ce su rage mutanen duniya su gusar da dukkan wasu addinai musamman addinin Musulunci daga nan su ɗaɓɓaka bauta wa shaiɗan."
Baya ga waɗannan akwai wasu tarin saƙonnin da ke zargin manyan masu kuɗin duniya kamar su Bill Gates da Ellon Musk da hannu a son rusa duniya ta hanyar yi wa mutane rigakafin cutar.
Kuma ga dukkan alamu sun yi tasiri wajen saka shakku a zuƙatan mutane kan ko za su bari a yi musu allurar a lokacin da aka fara yin ta a Najeriya ko a'a.

Da gaske rusa Musulunci da Musulmai ake son yi?

Asalin hoton, Middle East Eye
Dangane da batun da ake yaɗawa na cewa rushe Musulunci da Musulmai ake son yi, BBC ta tuntuɓi wani fitaccen malamin addini a Najeriya Dr Mansur Sokoto, kan yadda yake kallon lamarin, inda ya ce bai kamata mutane su dinga yaɗa abin da ba su da tabbaci a kai ba.
Sheikh Dr Sokoto ya ce matsayarsa a nan ita ce a miƙa wannan batu ga masanan ɓangaren kimiyya.
"Ƙwarai ya kamata malaman addini su bayar da fatawa amma sai bayan sun zauna da masana kimiyya sun fayyace musu komai.
"Kamata ya yi kamar yadda muka yi ta rubutu lokacin ɓullar cutar, yanzu ma kwamitin malamai a Najeriya sai su fitar da bayanai ga al'umma bayan gamsuwa da bayanan masana kimiyya.
"Muna buƙatar mu san yaya riga-kain kee aiki, mece ce illarsa da tasirinsa, daga nan sai mu fitar da matsaya a kai," in ji malamin.
Dr Sokoto ya kuma ce akwai matsalar da ake fama da ita na wasu masu faɗa da duk abin da kimiyya ta zo da shi gaba ɗaya.
Waɗannan maganganu na cewa tuggu ne sun yi yawa dole sai an zauna an fayyace yadda za a shawo kansu, a cewar malamin.
"Ni a yanzu ba ni da wata matsayar da zu iya yayatawa. Ina kira ga malaman addini da su haɗa kai su fitar da fatawa.
"Batun a yi ko kar a yi ba namu ba ne mu kaɗai, sai mun yi bincike na ƙwarai tare da la'akari da waɗanda ake binciken a kansu."
"Duk masu magana a kan batun da masu yaɗa maganganu ba masana ba ne.
"Mutane kuma suna son yaɗa labari da suka danganci haka, a dinga cewa ai so ake a kashe mu, so ake a ƙarar da mu, shi ya sa masu shirya irin waɗannan bayanai ke karkata ga hakan," kamar yadda malamin ya ce.
Ga wani bidiyon da Sheikh Dr Ahmad Mahud Gumi kuma ke bayani kan halaccin riga-kafin ko da an haɗa shi da sinadaran da haramun ne cin su a Musulunci.
Wasu manyan duniya da ƙasashen da suka fara allurar
Tuni dai wasu manyan masu faɗa a ji na duniya suka karɓi wannan allurar riga-kafin kamar su Yarima mai jiran gadon Masarautar Saudiyya Muhammad Bin Salman, wanda Musulmi ne kuma shugaban masarautar da ta zam tushen Musulunci.
Akwai irin su zaɓaɓɓen shugaban Amurka Joe Biden da Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da mataimakin shugaban ƙasar Amurka Mike Pence da Fira Ministan Kuwait Sheikh Sabah Khaled Al-Hamad Al-Sabah, wanda shi ma Musulmi ne.
Ƙasashen da aka fara allurar:
- Saudiyya
- Kuwait
- Qatar
- Amurka
- Faransa
- Jamus
- Burtaniya
- Costa Rica
- Chile
- Ajantina
- Rasha
- Canada
- Serbia
- Slovakisa
- Switzerland
- Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE
- Belarus
- Spaniya
- Romaniya
- Poland
- Oman
- Mexico
- Malta
- Italiya
- Isra'ila
- Hungary
- Girka
- Denmark
- Cyprus
- Czech Republic
- Crotia
- Belgium.

Yaya mutum yake ji bayan an yi masa allurar?
Dr Madigawa wanda tuni aka yi masa allurar ta farko kuma za a yi masa ta biyun ranar 20 ga watan Janairun 2021, ya ce tun da aka yi masa allurar bai ji wani illarta ba ta kowane ɓangare a jikinsa.
"Garas nake jin kaina. Kuma dama ina son na shaida wa mutane cewa kowace irin allura ko magani kan yi wa wasu mutane ƴar ƙaramar illa, abin da ake kira side effect.
"Amma dai za ka gwammace sau 100 gara wannan ƴar ƙaramar illar ta maganin fiye da kamuwa da cutar."
Likitan ya ƙara da cewa kamata ya yi a ce gwamnati ta yi isasshiyar faɗakarwa kan muhimmancin wannan allura da duk wani bayani da ya shafe ta.
"Bai kamata ma a ce gwamnati ta bar irin waɗannan miyagun mutane suna yaɗa bayanai munana na ƙarya a kan allurar ba.
"Hakan zai sa su yi nasara wajen cusa tunanin da bai dace ba a zuƙatan mutane," a cewar Dr Madigawa.












