Iran ta fara gwajin allurar riga-kafin Covid-19 da ta haɗa

Tayebeh Mokhber, wadda ƴar wani babban jami'in gwamnati ne mai suna Mohammad Mokhber ce, ta kasance mutum na farko a kasar da aka yi wa allurar

Asalin hoton, EPA

A karon farko Iran ta fara gwajin riga-kafin cutar korona da masanan ƙasar su ka hada, inji kafofin yada labarai na cikin gida.

Tayebeh Mokhber, wadda ƴar wani babban jami'in gwamnati ne mai suna Mohammad Mokhber ce, ta kasance mutum na farko a kasar da aka yi wa allurar a cibiyar bincike ta Cov-IranBlessing ranar Talata.

"Wannan sako ne ga al'ummar Iran cewa mun amince da sahihancin abin da mu ke yi wa jama'armu allura, kuma idan akwai wata matsala, to mu da iyalanmu mun amince da haka," inji ministan lafiya Saeed Namaki a wata hira da aka yaɗa ta tashar talabijin mallakin gwamnatin Iran.

A daya bangaren, Mista Mokhber ya sanar da cewa cikin makonni masu zuwa, kasar za ta iya samar da alluran riga-kafin miliyan dya da rabi a kowane wata.

Kusan Iraniyawa 55,000 ne suka mutu sanadiyyar cutar ta korona - wadda wannan ne lakaluma mafi yawa na mamata daga cutar a fadin Gabas ta tsakiya - inda kawo yanzu fiye da mutum miliyan 1.2 suka harbu daga kwayar cutar.

Shugabannin Iran sun dade suna cewa takunkuman da Amurka ta kakaba wa kasarsu na hana su damar sayo magungunan riga-kafin, duk da cewa takunkumin bai shafi magunguna da kayan agaji ba.

Iran ta rattaba hannu kan wani shiri na Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya mai suna Covax, wanda a karkashinsa za a tabbatar kasashe masu fuskantar matsalolin tattalin arziki a fadin duniya sun sami alluran riga-kafin.