Rigakafin Coronavirus: Coge da kutungwila sun mamaye nemo maganin cutar

Asalin hoton, EPA
- Marubuci, Daga Gordon Corera
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan tsaro
Lokacin da Rasha a ranar 11 ga Agusta ta sanar da samar da rigakafin korona da ta kira da sunan Sputnik V, wani saƙo ne da ba za a yi watsi da shi ba.
A shekarun baya 1957, Daular Soviet ta ƙaddamar da tauraron Sputnik kuma ta sha gaban kowa. Yanzu kuma Rasha tana ikirarin shata iyaka kan kimiyar lafiya.
Amma masu sukar na iƙirarin tana matsawa da yawa. Kuma shakkun da wasu suke da shi bayan sanarwar, wata tunatarwa ce ga hamayya tsakanin ƙasashen duniya.
A wannan hamayya, akwai masu zargin ana bin dubaru da leƙen asiri da ɗaukar kasada da kuma hassada yayin tattauna "kishin ƙasa kan batun rigakafin."
Rigakafin korona yanzu ta kasance wani abu mai daraja da kuma ake nema ido rufe bayan ƙokarin likitoci a wannan zamanin. Ba wai don ceton rai ba, amma wani ƙwarin guiwa ne ga kawo ƙarshen wannan yanayi da kuma nasara ga waɗanda suka tsira.
"Ban taɓa ganin yadda siyasa kan harakar magani ta yi muni ba," in ji Lawrence Gostin, farfesan dokokin lafiya a duniya a Jami'ar Georgetown da ke Amurka.
"Dalilin shi ne yadda batun samar da rigakafin korona ya koma wata siyasa inda manyan ƙasashe suke ganin rigakafin wani babban tasirin siyasarsu ne ga mamayar kimiyar lafiya wanda zai tabbatar da tsarinsu a matayin wanda ya fi na kowa.
A halin yanzu akwai kusan rigakafin shida da ake jiran tabbatar da ingancinsu a Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da suka ƙunshi uku a China, ɗaya a Birtaniya, ɗaya a Amurka da kuma na haɗin gwiwa tsakanin Jamus da Amurka
It is not hard to develop a vaccine - it's hard to prove a vaccine is safe and effective
A ka'ida a kan ɗauki shekaru kafin a samar da rigakafi. Kuma yayin da ake ta hanzarin samarwa, rigakafin Rasha Sputnik ya haifar da shakku kan bin dubarun sauƙaƙa tsarin da aka saba.
A watan Yuli, Birtaniya da Amurka da Canada sun zargi hukumomin leƙen asirin Rasha da yin kutse ga bincikensu na rigakafin, wani abin da gwamnatin Kremlin ta musanta.
Zargin daga majiyoyin leƙen asiri a lokacin shi ne satar bayanai maimakon lalata su.
Daga baya, ma'aikatar shari'ar Amurka ta zargi China da yin kutse ga aikinta samar da rigakafin. China kuma ta fito ta musanta zargin na Amurka tana mai cewa ita ta ma taimaka wa wasu aminanta na ƙasashen waje da wasu bayanai game da annobar.
Babbar damuwar ita ce kauce wa wasu hanyoyin da ke kawo jinkiri ta hanyar tabbatar da ingancin magani.
"Akwai hanyoyin da yawa da ake kauce wa, musamman kan batun Rasha," inji Thomas Bollyky daraktan shirin kiwon lafiya na duniya a majalisar hulɗar kasashe. "ba wahala ba ne samar da rigakafi. Amma tabbatar da ingancinsa ne ke da wahala, kuma idan ƙasashe kawai abin da ya dame su su samar da rigakafin za su iya kauce wa hanyoyin tabbatar da ingancinsa."
Matakin Rasha na yi wa maganinta Sputnik rijista kafin babban gwajin tabbatar da shi ba tare wallafa bayanan bincikenta ya haifar suka daga ƙasashen yammaci.
Dr Anthony Fauci, ɗaya daga cikin sanannun mambobi a kwamitin yaki da korona a fadar White House, ya ce "Yana shakku" ko Rasha ta tabbatar da ingancin maganinta, rashin illarsa da ƙarfinsa.
A Moscow an ɗauki wannan shakkun da ake bayyanawa a matsayin "hassada". Waɗanda suka samar da rigakafin sun ce ba da daɗewa ba za su wallafa bayanan bincikensu ga mujallar lafiya ta duniya.
Yayin da kuma China ta yi saurin tattara ci gabanta.

Asalin hoton, O’Neill Institute
Haifar da fargaba kan rigakafi
Diba da girman buƙatun jama'a kan rigakafi, shin bai dace a ɗan yanke wasu hanyoyi ba da ake tunani?
Rashin saka rigakafi a matsayin gwaji, tare da gaggawar fitar da shi, zai haifar da wani babban ƙwarin-guiwa ga jama'a wanda kuma zai ƙara yaduwar cutar korona. Duk maganin da daga baya aka gano yana da illa, zai iya haifar da wata fafutikar adawa da shi.
Yawancin aikin samar da rigakafi na kasuwanci ne kuma tare da haɗin guiwar kasashen duniya. Amma wannan bai hana wa gwamnatoci ɗaukarsa ba a matsayin wata alama da alfahari da nuna ƙarfin kimiya da kuma nuna wa duniya yadda suka kawo ƙarshen rikicin.

Asalin hoton, Getty Images
"Abin da ya ja hankalin ƙasashe su dinga hamayya kan samar da rigakafi yawanci damuwa ce ta buƙatun cikin gida musamman domin nuna yadda suka ɗauki yaki da wannan annoba da muhimmanci," inji Mr Bollyky.
Gwamnatin Trump a Amurka na fuskantar matsin lamba a yayin da ƙasar ke tunkarar zabe. Kamar Rasha ba za ta ji kunyar kwatanta maganinta ba wanda ta kira Operation Warp Speed - wato wani shirin talabijin da ake nuna Star Trek.
A Birtaniya, maganin da aka samar a cikin gida zai ƙara wa gwamnatin Firaminista Boris Johnson farin jini wadda ta fuskanci ƙalubale.
Sakataren harakokin kiwon lafiya, , Matt Hancock, ya ce "Birtaniya na ci gaba da jagorantar duniya" kan samar da rigakafi. Akwai wasu rigakafin da Birtaniya aka amince ta saya don ta yi gwajin ingancinsu don gudun kada su kasance wasu ne suka yi nasara. Amma wannan ya haifar da shakku kan wani ɓangare na hamayyar.
Rigakafin kishin kasa
"Tabbas akwai rigakafi na kishin kasa tsakanin ƙasashen yammaci," in ji Thomas Bollyky. "Tsarinsu… kamar yadda ake gani a Amurka da Birtaniya shi ne samar da magani da dama na rigakafin."
Tabbas, kishin ƙasa na ci gaba tun kafin cutar korona ta kutso, amma cutar ta ƙarfafa wannan.
An ga yadda ƙasashe ke rige-rigen samun na'urar numfashi da kuma kayayyakin kariya kowa na neman ya sha gaban wani ya nuna yadda ake dogaro da wasu ƙasashe wanda kuma ya haifar da ƙara bunƙasa na gida.
Game da samar da rigakafi domn raba wa a duniya, waɗanda suka fara samarwa dole su mayar da hankali ga ceton rayuka da farfaɗo da tattalin arziki, haka kuma gaza samar da maganin zai haifar da fushi tsakanin jama'a da ɗiga alamar tambaya kan cancanta.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya sake yin kira a ranar 18 ga Agusta ga ƙasashe masu arziki su taimaka wa ƙasashe matalauta da maganin rigakafi. "muna bukatar kauce wa rigakafin kishin kasa" inji shi.
Kasancewa na farko da ya fara sayar da rigakafin a kasuwa ba lalle ya kasance rigakafin shi ne ya fi ƙarfin inganci kuma masana sun bayyana shakku cewa wannan ba hamayya ba ce a samu jagora ɗaya da ya kammala.











