Coronavirus: Abu hudu game da riga-kafin da Najeriya ta karɓa

rigakafin Korona

Asalin hoton, Getty Images

Najeriya ta karbi alluran riga-kafin cutar korona a ranar Talata domin yi wa 'yan kasar.

Najeriya ta kasance kasa ta uku a yankin Afrika Ta Yamma da suka ci moriya tallafin alluran riga-kafin karkashin shirin COVAX, baya ga Ghana da Cote D'Ivoire.

Shugaban Hukumar Kiwon Lafiya a Matakin Farko a Najeriya NPHCDA, Dr. Faisal Shuaib ya ce sun shirya tsaf riga-kafin da kuma yi wa ƴan Najeriya da suka fi buƙatar a yi musu allurar.

Ya ce tuni har sun fara horar da ma'aikatan lafiyar da za su yi aikin.

Adadin yawan riga-kafin

Allurar rigakafi kusan miliyan huɗu aka ba Najeriya daga wani ɓangare na rigakafi miliyan 16 da shirin COVAX ya tsara ba kasar.

Shirin Covax ya shafi tabbatar da kowace kasa a duniya ta samu nata kaso na rigakafin korona.

Wannan kaso ne na farko da Najeriya za ta karɓa daga cikin miliyan 16 da za ta samu ƙarƙashin inuwar Covax a watanni masu zuwa.

Nau'in riga-kafin da Najeriya za ta karɓa

Allurar riga-kafin Oxford ta AstraZeneca Najeriya ta karɓa a ranar Talata.

Manyan ƙasashe kamar Jamus da Faransa suna amfani da riga-kafin amma ana yi wa ƴan shekara 18 zuwa 64 saboda rashin bayanai kan ingancin allurar ga waɗanda suka haura shekara 65.

Wata sanarwa ta haɗin gwiwa daga NPHCDA da Hukumar Lafiya Ta Duniya da kuma UNICEF ta ce za a kawo riga-kafin ne daga Indiya.

Wa za a fara yi wa riga-kafin?

Za a fara yi wa ƴan Najeriya da suka fi zama cikin hatsarin harbuwa da cutar inda za ta fara da ma'aikatan lafiya.

Gwamnatin ƙasar kuma ta ce ta tsara yi wa akalla kashi 70 na ƴan Najeriya da suka cancanci a yi musu riga-kafin wato wadanda shekarunsu suka kama daga 18 zuwa sama a cikin shekaru biyu.

A bana Najeriya na fatan yi wa kashi 40 na ƴan kasarta rigakafin da kuma kashi 30 a 2022.

Ya kuma kara da cewa su ma rumbunan da za a adana alluran masu bukatar yanayi na tsananin sanyi an kammala hada su a dukkan matakai.

Kasashen Afirka da suka karɓi riga-kafin

Covax

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ghana da Ivory Coast sun karɓi riga-kafin korona ƙarƙashirin tsarin Covax

Ghana da Ivory Coast sun riga Najeriya samun riga-kafin daga shirin na COVAX kuma tuni suka fara yi wa ƴan kasarsu.

Shugaban Ghana Nana Akuffo Addo ya kasance mutum na farko a kasar da aka fara yi wa allurar riga-kafin korona.

An yi wa shugaban allurar ne a ranar Litinin a wani asibitin soji da ke birnin Accra tare da mai dakinsa; kafin mataimakinsa da mai dakinsa da sauran manyan jami'an gwamnati.

A ranar Litinin ne a Ivory Coast aka fara yi wa mutane rigakafin cutar ta Corona bayan karbar magungunan daga shirin na COVAX.

Ma'aikatan lafiya ne rukunin farko da za a fara yi wa riga-kafin daga cikin allura dubu 500 da kasar ta samu.

COVAX dai wani shirin ne da wasu hukumomi da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ke shugabanta da manufar tabbatar da su ma mataulautan kasashe ba a bar su a baya ba wajen samun riga-kafin wannan annobar da ta game duniya.