WHO za ta hukunta jami'an da suka ci zarafin mata a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo

Cin zarafin sun faru ne tsakanin shekarun 2018 zuwa 2020

Asalin hoton, Getty Images

Wani sabon rahoto da aka fitar, ya nuna ma'aikatan Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, na daga cikin ma'aikata 83 da ake zargi da cin zarafin mata da 'yan mata ta hanyar lalata da su a lokacin da suke aikin dakile barkewar cutar Ebola a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo.

Cin zarafin da ya hada da zargin aikata fyade guda tara, ma'aikatan kasashen wajen da na cikin gida suka aikata su tsakanin shekarun 2018 da 2020.

Rahoton ya fito ne bayan sama da mata 50 sun shigar da korafin an ci zarafinsu.

Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce babu wata hujja ta aikatawa matan hakan.

Wannan rahoto mai dauke da shafi 35, wata hukuma mai zaman kanta ce ta gudanar da binciken da tattara bayanai.

Hukumar ta zanta da gwamman mata daban-daban, wadanda suka yi zargin an yi musu tayin ba su aiki, amma kuma su ba da kansu a matsayin lada, kuma 21 daga cikin ma'aikatan 83 ma'aikatan WHO ne.

Yayin da matan kauyuka kuma aka dinga yin lalata da su, bayan an dirka musu barasa, wasu kuma kwantan bauna ake musu a kan hanya, ko a asibiti, ko kuma a tilasta su aikata lalatar inda biyu daga cikinsu suka samu juna biyu.

Tuni WHO ta sanar da korar ma'aikata hudu da rahoton ya ambata, tare da alkawarin daukar matakan da suka dace.

Da ya ke jawabi a wani taro Dakta Tedros, ya ce rahoton mai tayar da hankali ne tare da ba da hakuri ga wadanda lamarin ya shafa.

"Ina mai ba ku hakuri kan abin da ma'aikatanmu suka aikata a gare ku, wanda kamata ya yi su ba ku kariya, alhaki ya rataya a wuyana, na tabbatar da an hukunta wadanda aka samu da laifi, ba su da wani abu da za su kare kansu da shi."

Ya kara da yin alkawarin tallafa wa matan da suka fuskanci cin zarafin, tare da alwashin yin garanbawul kan yadda WHO ke gudanar da ayyukanta.

Ita ma daraktar WHO a Afirka, Matshidiso Moeti, ta nemi afuwar mutanen, inda ta ce "Saboda abin da ma'aikatanmu suka aikata, abin bakin ciki, da tashin hankali, da karya zuciyar wanda aka aikata hakan a gare shi."

A karshe hukumar da ta gudanar da binciken ta ce, ta gano gazawa wajen hukunta wadanda ake samu da laifin aikata cin zarafi ta hanyar lalata.

Watakila hakan ya faru ne sakamakon mayar da hankali baki daya kan kan yadda za a magance matsalar yaduwar cutar Ebola, wanda hakan ya sanya masu aikata laifin cin karensu babu babbaka.

A wancan lokacin sama da mutum 2,000 cutar Ebola ta hallaka a Jamhuriyyar Dimukradiyyar Congo.