Malaria: Yadda ake fama da ƙarancin maganin cutar a Jigawa

Sauro

Duk da yake, yanayin sanyi ya kankama a sassan Najeriya, zazzaɓin cizon sauro na ci gaba da yin mummunar illa a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin kasar.

Ƙanana da manyan asibitocin jihar kan cika maƙil a kowacce rana saboda yawan marassa lafiyan da ke tururuwa don neman magani.

Lamarin dai ya fi shafar ƙananan yara da mata masu juna biyu waɗanda a wasu lokutan kan zo da rashin jini a jika ko kuma suma.

Iyayen yaran da suka kamu da cutar sannan kuma suka kai su asibiti sun yi korafin cewa duk da yake gwamnatin jihar ta bayar da magungunan cutar zazzabin cizon sauron kyauta don a rabawa mutane, su basa samu.

Wani mahaifin wata yarinya da ta kamu da cutar ya shaida wa BBC cewa, ya samu wasu magungunan kyauta amma kuma da yawa daga cikin wadanda likita ya rubuta musu shi ya siya da kansa kuma ya kashe makudan kuɗaɗe kafin 'yar tasa ta warke.

Marassa lafiya da dama da BBC ta tattauna da su sun ce ba wani abu ke damunsu ba illa rashin isassun magunguna a asibitocin jihar da kuma ƙarancin gadajen kwanciya.

Kazalika cutar kuma a wannan karon tazo da wani sabon salo wanda ba a taba gani ba a wannna shekarar inda yawancin wadanda suka kamu da cutar ta maleriya a kan same su da karancin jini wasu kuma har ta kan kai su ga suma ko jijjiga.

Ba kasafai ake kamuwa da cutar maleriya a lokacin sanyi ba saboda sauron shi kansa ba ya tasiri saboda sanyi, amma a wannan karon batun ya sauya.

Me yasa ake kamuwa da cutar maleriya a lokacin sanyi?

Masana a bangaren kiwon lafiya sun yi bayani a kan dalilin da ya sa ake kamuwa da cutar maleriya a lokacin sanyi, Dakta Kabir Ibrahim,kwararre ne kan kula da lafiyar al'umma ya kuma shaida wa BBC cewa,

"Kwayar cutar maleriya a wasu lokutan kan rikiɗa inda lokaci-lokaci sai aga ta fito da wasu irin halitta wanda yake bijirewa magungunan da aka saba da su na yau da kullum".

Likitan ya ce a wasu lokuta kuma mutane suke haddasa duk wata matsala wajen kamuwa da maleriya saboda basa kiyayewa da ƙa'idojin da aka gindiya na kiyayewa.

Don haka Dakta Kabir Ibrahim ya yi kira ga iyaye da su rinka kiyayewa da duk wasu ƙa'idoji da aka shimfiɗa musu.

Karin Bayani

Ba a jihar Jigawa kaɗai ake fama da wannan cuta ta maleriya ba, kusan jihohin Najeriya na fama da wannan matsalar ta cutar maleriya.

Hukumar Lafiya ta Duniya dai ta ce cutar zazzabin cizon sauro ita ce ta ɗaya wajen kashe ƙananan yara a Afirkam kuma idan har aka samu mutum huɗu sun kamu da cutar to ko shakka babu ɗayansu a Najeriya ya ke.