Zazzaɓin Maleriya ya zaburar da ni samar da sabulun da ke maganin sauro

Matar da ta samar da sabulun wankan da ke maganin sauro

Asalin hoton, Joan Nalubega/Facebook

Wata 'yar kasuwa a Uganda wadda yanzu ta shahara a bangaren sana'arta har ma ta samu lambobin yabo, ta shaida wa BBC cewa yadda ta sha fama da cutar zazzabin cizon sauro tana yarinya ne ya zaburar da ita har ta yi tunanin samar da wani abu da zai maganin sauron.

Joan Nalubega, wadda ta girma a gidan marayu, ta samar da sabulun wanka na gargajiya da zai rinka maganin sauro da ma kasheshi idan har ya hau jikin mutum.

Ta ce, "A shekarar 2016, na fahimci cewa abubuwan da mutane ke amfani da su na gargajiya, sune wadanda aka jima ana amfani da su shekara aru-aru, suke kuma yi mana magani".

Ms Nalubega, ta ce "Baya ga yadda cutar zazzabin cizon sauro ta wahalar dani, na kuma fahimci cewa cutar na matukar yaduwa musamman a yankunanmu na karkara duk da kokarin da gwamnati ke yi wajen wayar da kai da kuma bayar da tallafi don kare kai daga kamuwa da cutar".

Ta ce, yawanacin mutane na amfani sosai da shawarwarin da gwamnatin ta basu kamar amfani da gidan sauro da dai makamantansu, amma duk da haka ana kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro inji ta.

Matashiyar ta ce sabulun data samar za a iya amfani dashi a kowacce rana.

Yana nan a ko ina a kasuwa da shaguna da asibitoci, kuma farashinsa ba bu yawa ta yadda kowa zai iya siya don amfani inji ta.

Wannan kokari nata ya janyo mata daukaka inda har ta kai wani mataki na samun kyautuka da kuma lambobin yabo daga kungiyoyi daban-daban.