Coronavirus: Hanyoyi uku da za ku bambance maleriya da cutar korona

Asalin hoton, Getty Images
Mene ne alamomin waɗannan cutukan biyu (zazzabin cizon sauro da cutar korona), hanyoyin kamuwa da su da hanyoyin magance su da hanyoyin kare kai daga kamuwa da su?
Sannan waɗanne abubuwa ne a tsakanin waɗannan cutukan biyu da ke kamanceceniya?
Zazzaɓin maleriya da cutar korona: cutuka biyu masu kamanceceniya
A wata hira da BBC, Farfesa Sylvie Audrey shugaban Hukumar da ke yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Senegal, ya tabbatar da cewa cutar korona da zazzaɓin maleriya na da alamomi da dama da suke kama.
'Misali, ana samun zazzaɓi a cutukan biyu da kasala da ciwon kai.
Amma akwai wasu alamomi da ake samu a masu fama da cutar korona kamar sarƙewar numfashi wanda masu fama da zazzaɓin maleriya ba sa samu.

Asalin hoton, Getty Images
Haka kuma ya ce alamomin mura na daga cikin manyan alamomin da ake gani a masu fama da cutar korona.
Sannan sarƙewar numfashin kan zo ne idan cutar ta yi nisa. Amma kuma, ana samun sarƙewar numfashi ma idan maleriya ta yi tsanani a jiki.
Dakta Audrey ya ce abin da ya fi dacewa shi ne da an ji waɗannan alamomi a tafi asibiti.
1. Kwayoyin cutar da ke janyo cututtukan biyu sun bambanta
A likitance, ƙwayoyin cutar da ke janyo maleriya da cutar korona sun bambanta. Ƙwayar cutar virus ce ke janyo cutar korona yayin da ƙwayar cutar parasite ce ke janyo maleriya.

Asalin hoton, Getty Images
Maleriya ta kama mutum miliyan 219 sannan ta janyo mutuwar mutum 435,000 a shekarar 2017, kuma ta kasance cutar da ta fi ko wacce shafar mata masu ciki da ƙananan yara ƴan ƙasa da shekara biyar.
Kashi 80 cikin 100 na waɗannan mutanen na rayuwa ne a ƙasashe goma sha biyar a yankin Afrika kudu da hamadar sahara a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO.
Ana yaɗa ƙwayar cutar maleriya ne idan macen sauro ta ciji mutum yayin da COVID-19 kuwa sabuwar ƙwayar cutar korona ce janyo ta.
Ba a taɓa ganin wannan sabuwar ƙwayar cutar korona ba kafin ɓarkewar annobar a watan Disambar 2019 a birnin Wuhan na China.
Kawo yanzu, annobar ta shafi ƙasashe da dama a faɗin duniya.

Asalin hoton, Getty Images
Ranar 11 ga watan Maris na 2020, WHO ta ayyana cutar a matsayin annobar duniya sannan ta yi kira a ɗauki tsauraran matakai din daƙile ta: wato killace kai a gida, daina musabiha, shiga taro, rage tafiye-tafiye da kuma yawan wanke hannu.

Asalin hoton, Getty Images
2. Hanyoyin yaduwar maleriya da cutar korona
Hanyoyin da cututtukan nan ke yaɗuwa sun bambanta a cewar Dakta Adjé Clément na asibitin koyarwa na Treichville da ke Côte D'Ivoire.

Asalin hoton, Getty Images
Ya bayyana wa BBC cewa maleriya na yaɗuwa ne idan macen sauro nau'in genus Anopheles, wadda ita ma ta samu cutar bayan namijin sauron ya cije ta, ta ciji mtum sannan ta sa masa ƙwayar cutar.
Ƙwayar cutar na kama ƙwayoyin halittar dan Adam da ke hantarsa sannan ta bi jini, ta shiga cikin ƙwayoyin jin na red blood cells ta lalata su.
Dangane da cutar korona kuwa, Dakta Adje ya ce "Ana yaɗa cutar ne idan kwayoyin cutar suka watsu ta hanyar atishawa ko tari.

Asalin hoton, Getty Images
3. Magani

Asalin hoton, Getty Images
Akwai hanyoyin magani idan mutum ya nuna alamomin cutar korona.
Kawo yanzu, babu wani taƙamaiman maganin cutar korona. Sai dai a sha maganin zazzaɓi da ciwon jiki da cutar ke haifarwa.
Amma masu bincike da dama a faɗin duniya na nan suna aiki tuƙuru wajen gano riga-kafinta.
Idan cutar ta yi tsanani a jiki, ana iya ba marar lafiyar magungunan antibiotic ko kuma a sa masa na'urar numfashi ta ventilator.
Zazzaɓin maleriya kuwa na da magani kuma ana iya samunsa a ko ina.











