An gano kwayar halitta mai maganin zazzabin cizon sauro

mosquito

Asalin hoton, Getty Images

Masu bincike daga Kenya da Birtaniya sun gano wata kwayar halitta da suka ce na da gagarumin muhimmanci wajen magance zazzabin cizon sauro.

Binciken da aka wallafa shi a wata mujallar kimiyya mai suna Nature Communications, ya gano cewa wannan kwayar halittar na iya kawo karshen barnar da sauro kan yi a kasashe masu zafi.

Masu binciken sun kuma gano kashi biyar cikin dari na sauron da ke gabar tafkin Victoria a Kenya na da wata kwayar halitta a jikinsu mai suna Microsporidia.

Cikin sauron da ke da wannan kwayar halittar, ba su gano ko da daya da ke dauke da kwayar da ke haddasa zazzabin cizon sauron ko maleria.

Masu binciken na shirin saka wa sauro da Microsporidia, kuma daga baya sai su sake su su shiga cikin 'yan uwansu - matakin da suke fatan zai zama sanadin kwayar halittar ta bazu cikin jinsin sauron wadanda matan cikinsu ne ke baza zazzabin cizon sauron yayin da suke shan jinin dan Adam.

mosquito net

Asalin hoton, Getty Images

Jeremy Herren shi ne ke jagorantar masu binciken a Cibiyar Kasa da kasa ta Binciken Yanayin Kwari a Nairobi:

"Mun gano cewa akwai wata halitta da ake samu a jikin wasu dag cikin sauro masu haddasa zazzabin malaria, kuma mun gano cewa halittar na dode samar da kwayar halittar da ke janyo cutar ta malaria gaba dayanta."

"Wannan dai zai kasance muhimmain ci gaba, kuma abin da muke son yi shi ne gano hanyar da zamu kara yawan sauron da ke dauke da kwayar halittar", inji shi.

Idan wannan binciken yayi nasara, to zai taimaka wajen rage yawan mace-macen da zazzabin maleriya kan haddasa musamman tsakanin yara masu kananan shekaru da yawansu ya zarce 400,000 a kowace shekara.