Afghanistan: Zuba jari muke buƙata a Afirka, ba sojojin yaƙi ba – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Buhari ya ce "dakarun aiki Afirka ke buƙata daga Amurka da Turai ba na yaƙi ba"

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa nahiyar Afirka "zuba jari da ayyukan yi" take buƙata ba sojojin yaƙi da ta'addanci ba na ƙasashen Yamma.

Duk da cewa shugaban ya yarda Afirka na da isassun sojojin da za su yaƙi ta'addanci, ya ce nahiyar na buƙatar kayan aiki na zamani daga ƙasashen Amurka da Turai.

Cikin wata maƙala da ya rubuta wa jaridar Financial Times ranar Lahadi da ake wallafawa a Birtaniya, Buhari ya jaddada cewa ficewar Amurka daga Afghanistan ya nuna cewa "ƙarfin soja zai iya rage wa ta'addanci ƙarfi amma zai iya dawowa bayan kawar da shi".

Kazalika, shugaban ya alaƙanta annobar korona da ƙaruwar hare-haren ta'addanci, yana mai cewa ta bai wa 'yan bindiga damar faɗaɗa hare-haren.

Maƙalar ta bayar da misali da ficewar dakarun ƙawance na ƙasashen duniya ƙarƙashin jagorancin Amurka daga Afghanistan bayan shafe shekara 20 suna "yaƙar ta'addanci", sai dai cikin kwana 10 ƙungiyar Taliban ta sake ƙwace iko da ƙasar.

'Ba sojoji muke buƙata'

Shugaba Buhari ya aminta cewa ta'addanci na ƙara ƙamari a Afirka musamman idan aka duba hare-haren masu iƙirarin jihadi a Mozambique da kuma ƙungiyar Al-Shabab a Somalia.

Sai dai ya jaddada cewa Afirka na da isassun dakarun soja da za su yaƙi irin waɗannan ƙungiyoyi.

"Bai kamata a tsammaci cewa Amurka da ƙawayenta na ƙasashen Turai za su ɗauki tsaron sauran ƙasashe da muhimmnanci ba kuma har abada. Afirka na da isassun dakaru na kanta.

"Sai dai za a iya taimakawa da kayan aiki da bayanan sirri da tsare-tsare," in ji shugaban.

'Zuba jari da ayyukan raya ƙasa muke buƙata'

Kazalika, Buhari na ganin cewa akwai buƙatar cike wagegen giɓin da ke tsakanin yawan al'ummar Afirka da kuma haɓakar tattalin arziƙinta, wanda ya ce shi ne abin da nahiyar ke buƙata daga Amurka.

"Abin da muke buƙata daga Amurka shi ne cikakkiyar alaƙar kasuwanci domin rage girman giɓin da ke akwai tsakanin yawan al'umma da kuma ƙaruwar tattalin arziki.

"Abin da muka fi buƙata shi ne zuba jari a ayyukan raya ƙasa. Layukan dogo da sufuri za su samar da damarmaki ga waɗanda ba su da su.

"Duk da cewa ƙasashen Afirka shida daga cikin 10 da tattalin arzikinsu ke saurin haɓaka, haɓakar tattalin arzikin nahiyata ba shi da yawan da zai iya magance matsalar yawan al'umma.

"Tun bayan fara yaƙi da ta'adanci da Amurka ta ƙaddamar a 2001, al'ummar Afirka sun kusan ninkawa. Hakan na nufin cewa a kullum ana samun marasa aikin yi. Ƙarancin ƙwarin gwiwa ne babban abin da ke jawo shiga ƙungiyoyin ta'addanci.

'Ana zargi na da ɓarnata kuɗi kan gina layin dogo zuwa Nijar'

Wani batu da ya dinga jan hankalin 'yan Najeriya shi ne na gina titin jirgin ƙasa a yankunan ƙasar da gwamnatin APC mai mulki ke yi, wanda ta ce zai haɗe har da maƙociyarta Jamhuriyar Nijar.

Sai dai Buhari ya soki ra'ayin masu zargin cewa gwamnatinsa na ɓarnata kuɗi ne kawai, yana mai cewa suna yi ne domin samar da damar kasuwanci tsakanin ƙasashen da kuma ayyukan yi.

"Wannan dalilin ne ya sa muka fara gina layukan dogo daga kudanci zuwa arewa maso gabas zuwa Nijar, maƙociyarmu.

"Ana zargin gwamnatina da ɓata kuɗi saboda kasuwancin da ke tsakanin ƙasashen namu ba shi da girma. Amma wannan ba abin mamaki ba ne idan aka duba cewa babu hanyoyin sufuri na kasuwanci a tsakaninmu."

Presentational grey line

Shugaba Muhammadu Buhari bai gushe ba yana mai jadda cewa: "Afirka ba ta buƙatar takubba wajen yaƙi da ta'addanci, sai dai kayan aiki. Tabbas dakarunmu na buƙatar kimiyya da kuma bayanan sirri waɗnda ba su da shi.

"Amma dakarun da muke buƙata a nahiyar Afirka su ne na ayyuka, ba yaƙi ba."