‘Yaki da ta’addanci’: Shin ƙasashen Yamma sun daina tura sojojinsu ƙasashen waje?

US soldier sits in the rear of Chinook helicopter while flying over Kabul on 10 August 2017

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sojojin ƙasashen Yamma da suka rage a Afghanistan na barin ƙasar bayan shekara 20
    • Marubuci, Daga Frank Gardner
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan harkokin Tsaro

Sojojin ƙasashen Yamma na rige-rigen ficewa daga Afghanistan a watan nan. Faransa ta bayyana rage ayyukan soja a Mali. A Iraƙi kuma, sojojin Birtaniya da na sauran ƙasashen Yamma ba su da wata rawa da suke takawa a fagen yaƙi.

Shekara 20 kenan bayan da tsohon Shugaban Amurka George W Bush ya ƙaddamar da yaƙi da ta'addanci, ko hakan na nufin an daina tura sojoji fagen yaƙi zuwa ƙasashe masu nisa?

Ba yanzu ba tukunna - har yanzu akwai wasu sojoji da ke yaƙar masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel - amma ana sake tunani game da yadda waɗannan rundunoni ke aiwatar da ayyukansu.

Tura sojoji masu yawa da kuma shafe lokaci mai tsawo abu ne mai tsada sosai, musamman wajen kuɗi da lafiyar mutum da kuma matakai na siyasa a ƙasashen da suka tura su.

Yaƙin da sojojin Amurka ke yi a Afghanistan ya laƙume fiye da dala tiriliyan ɗaya - kwatankwacin fiye da naira tiriliyan 410 - da kuma dubban rayuka daga dukkan ɓangarorin.

Lokacin da yaƙin ke kan ganiya a 2010, sojojin Yamma sun kai 100,000. Bayan shekara 20, waɗanda suka rage suna ta ƙoƙarin barin ƙasar yayin da Taliban ke ƙoƙarin kama sabbin garuruwa da dama.

Gazawa

Irin yawan lokaci da kuma girman da shirin yaƙar masu ikirarin jihadi ke ɗauka shi ne yake ƙara nuna irin gazawar da za a samu.

Sojojin Amurka fiye da 58,000 ne suka mutu a Yaƙin Vietnam sannan sojojin Rasha kusan 15,000 suka mutu a Afghanistan - abin da ya sa aka yi saurin kawo ƙarshen waɗannan yaƙe-yaƙen kenan. Faransa ta yi asarar soja fiye da 50 a Mali tun daga 2013 kuma hakan ya sa Faransawa sun daina goyon bayan shirin.

A soldier of France's Barkhane mission stands next to children as he patrols in In-Tillit on November 1, 2017 in Mali

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Faransa ta shiga Mali tun a 2013

Sannan kuma akwai maganar kuɗin gudanarwa, wanda kusan ya fi ƙarfin duk wani abu da ake zato.

Lokacin da Saudiyya ta ƙaddamar da yaƙi a Yemen a 2015 ba ta taɓa tunanin za ta kai shekara shida tana yaƙin ba. An yi ƙiyasin Saudiyya ta kashe kusan dala biliyan 100.

Haka nan, yawan rasa rayuka ma kan hanzarta kawo ƙarshen yaƙi musamman a wurin da ba a yi tsammani ba.

Amurka ta sha kai wa taron biki hari, Saudiyya ma ta sha kashe fararen hula a Yemen da kuma take haƙƙin ɗan Adam waɗanda duk suke jawo wa ƙasashen asara ta abubuwa daban-daban.

Dangane da ƙasar Daular Larabawa wato UAE, labaran da suka ɓulla cewa sojojinta sun sha kulle fursunoni cikin kwantenoni har sai sun mutu, shi ne ya sa dole ta fice daga yaƙin na Yemen.

Kuma akwai yiwuwar sai dai gwamnatin ƙasar ta raba iko da ƙungiyoyin 'yan tawaye.

line

Babu wata tartibiyar amsa

A bayyane take cewa babu wata cikakkiyar amsa game da ƙasashen da suka gaza da kuma masu mulkin kama-karya. Bari mu duba misalai na baya-bayan nan:

  • A Iraƙi, 2003 zuwa yanzu: Harin da Amurka ta ƙaddamar tare da goyon bayan ƙasashen Yamma, da kuma mummunan yaƙin da ya biyo bayan hakan, ya sa 'yan siyasa sun daina tunanin ƙaddamar da yaƙi mai tsawo a Gabas ta Tsakiya.
  • Libya, 2011 zuwa yanzu: Matakin hana jirage tashi da ƙungiyar NATO ta ƙaddamar amma ba tare da sojoji a ƙasar ba, ya bai wa 'yan tawaye damar hamɓare Gaddafi daga mulki a 2011. Sai dai ƙasar ta afka cikin yaƙin basasa da kuma na masu iƙirarin jihadi, daga baya kuma ƙasashen Yamma suka yi watsi da ita.
  • Syria, 2011 zuwa yanzu: Tsoron da ƙasashen Yamma suka ji na shiga yaƙi tsakanin 'yan tawaye da kuma Shugaba Bashar al-Assad ya sa Rasha da Iran ta Turkiyya suka kankane al'amura. Shekara 10 kenan amma har yanzu ana faman zubar da jini.
  • Ƙungiyar Islamic State, 2011 zuwa yanzu: Wannan ne labari tilo mai cikakkiyar amsa wanda ƙasashe kusan 80 suka haɗa kai dom yaƙar ƙungiya maras imani da ke kiran kan ta Islamic State ko IS. Amma fa sai da aka shafe shekara biyar kuma yaƙin ya dogara ne da hare-hare ta sama da kuma ƙawance maras daɗi tsakanin ƙasashe. Yanzu haka IS na sake kafa sansano a Afirka.
  • Mali, 2013 zuwa yanzu: Dirar da sojojin Faransa suka yi ta taimaka wajen hana mayaƙan al-Qaeda da sauransu ƙwace birnin Bamako na Mali. Sai dai shekara takwas bayan haka, duk da kasantuwar sojojin haɗin gwiwa a ƙasar, yaƙin na ci gaba kuma shugaban Faransa ya nuna rashin jin daɗinsa ga shugabannin ƙasar da kuma yanƙurinsa na janye sojoji.

Muradina nan gaba

Saboda haka, idan babu sojojin da za a tura yaƙi zuwa ƙasashe masu nisa kuma na lokaci mai tsawo, to da me za a maye gurbinsu?

Shugaban Sojojin Birtaniya Janar Sir Mark Carleton-Smith ya ce: "Sojojin yanzu za su fi zama a dunƙule kuma za a fi saurin kai su wurare sannan suna tare ta hanyar intanet ta hanyar haɗa na'urar tauraron ɗan Adam da kowane soja a rundunar musamman ta Special Operations Brigade."

rage yawan sojojin ƙasa a fagen daga na nufin dogaro kan kimiyya da fasahar zamani da kuma ƙirƙirarriyar fasaha.

Yaƙin baya-bayan nan da aka yi tsakanin Azerbaijan da Armenia ya nuna yadda jirage marasa matuƙi, wanda Turkiyya ta samar, suka dinga tarwatsa tankokin Armenia kuma ba tare da masu kula da su sun ji ko ƙwarzane ba.

Yanzu haka sojojin haya sun fara dawowa fagen daga a Afirka, waɗanda a da ake ganin kamar an daina yayinsu.

Wani ƙwararre Dr Sean McFate ya ce "sabbin ayyukan da ƙasashe ke yi na ba su damar shiga yaƙi ba tare da sun shiga da kansu ba" ta hanyar tura sojojin haya.

Babban misali shi ne kamfanin Wagner Group na Rasha wanda ke aiki a wasu fagagen daga na Libya da Yammacin Afirka da Mozambique, duk da cewa tana musantawa.

Duk waɗannan ba sa nufin kawo ƙarshen tura sojoji yaƙi zuwa ƙasashe ƙetare. A Mali da Sahel, Faransa ka iya daƙile shirinta mai suna Operation Barkhane kuma ta mayar da sojojinta gida. Amma sojojin Majalisar Ɗinkin Duniya za su ci gaba da nasu aikin kuma na Faransar ma za su ci gaba da ayyuka ƙanana tare da sojojin haɗin gwiwa da ke yaƙi da ta'addanci.

A Iraƙi, sojojin NATO za su ci gaba zama domin horar da sojojin ƙasar da ke yaƙi da masu iƙirarin jihadi.

Sai dai kuma a Afghanistan, sojojin Yamma na tserewa a lokacin da aka fi buƙatar su fuskanci barazanar ƙungiyoyin Taliban da al-Qaeda da kuma IS.