Najeriya: Da tsadar kayan masarufi za mu ji ko da rage yawansu?

masarufi

Asalin hoton, Getty Images

Baya ga matsalolin da aka daɗe ana fama da su na tsadar kayan abinci da sauran su, yanzu haka wata babbar matsalar da ƴan Najeriya ke kokawa a kai ita ce, ta yadda aka rage yawa da nagartar akasarin kayayyakin amfanin yau da kullum.

Hakan kuma na faruwa ba tare da kuma raguwar farashinsu ba.

Cikin kayayyakin da matsalolin suka fi bayyana sun hada da irin taliyar nan ta cikin leda wato noodles da aka fi sani da taliyar yara, da madarar gari ta ƙananan ledoji, da su garin sabulu na wanki da na wanka, da markaɗaɗɗen tumaturin leda, har da su dunƙulen ɗanɗano da na leda.

Mutane suna ta bayyana takaici kan wannan yanayi da aka samu kai a ciki, inda batun ya zama abin tattaunawa a zauruka da dama na shafukan sada zumunta.

BBC Hausa ta zanta da mutane da dama daga kan masu sayen kayayyakin zuwa ƴan kasuwa da ke sayarwa don gano bakin zaren.

'Sun rage yawan kayayyakin'

Dukkan mutanen da BBC ta tattauna da su suna tambaya ne cewa da wanne za su ji, "da tsadar kayan masarufi za mu ji ko da rage yawansu," kamar yadda bakinsu ya zo ɗaya.

Wani magidanci da bai amince a bayyana sunansa ba ya shaida wa BBC cewa, a baya taliyar yara ta leda guda biyu takan ishe shi karin kumallo, amma yanzu haka sai an dafa masa uku zuwa hudu kafin ya ji ya ƙoshi.

''A da nakan ji na ƙoshi idan aka dafa min leda biyu na ɗan ɗora daffafe ko soyayyen ƙwai biyu a kai, amma a gaskiya abin mamaki leda biyu ko kusa ba ta ƙosar da ni saboda an rage yawanta sosai, ga kuma farashi ya ƙaru,'' in ji shi.

Haka ita ma Malama Hafsatu Bello a hirarta da BBC, ta bayyana cewa leda ɗaya ta taliyar ake dafa wa kowanne a cikin ƴaƴanta idan suka buƙata, amma yanzu sai daya da rabi ce take isar su.

''Ban ankara ba sai in ji suna faɗa min ba su ƙoshi da taliyar ba, sai da na lura na ga girmanta ya ragu sosai, kuma ga shi ba su rage kuɗin ba sam,'' in ji ta.

"Ba taliyar yara ce kawai ake wa wannan ƙwangen ba, wallahi hatta da sinadarin ɗanɗano na miya da man goge baki da sabulu da garin sabulu na wanki da madara da sauran kayan shayi, kai abubuwan ba za su lissafu ba wallahi," a cewar Hajiya Fauziyya Husaini, wata mazauniyar Kano.

Wannan layi ne

Wasu labaran masu alaƙa

Wannan layi ne
Bayanan bidiyo, Kalli wannan bidiyon da ya yi duba kan hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya

Ta ina abin ya samo asali?

BBC ta yi hira da ƴan kasuwa da dama a babbar kasuwar sayar da kayan masarufi ta Singer da ke birnin Kano a arewacin Najeriya, kuma duk bakinsu ya zo ɗaya cewa batun rage yawan kayayyaki babu ja a ciki.

Ɗaya daga cikinsu Malam Ibrahim ya ce "ko mu ƴan kasuwa mun shaida hakan.

"Masu sayen kayayyakin masarufi da dama suna dawowa su koka mana game da hakan da zarar sun koma gida sun lura an rage yawan kayayyakin da suka saba saye.

''Akwai waɗanda bayan sun sayi kayan za ka ga sun dawo mana da su su ce sun fasa saye, ko kuma mata za su zo su ce suna rigima da mazajensu a kan cewa ko an ba su shinkafa da ba ta cika ba, ko sun rage kuɗin cefane,'' in ji ɗan kasuwar.

Ya kuma ƙara cewa "saboda duk mutumin da za ka sayar masa da kaya kai ɗan kasuwa suka sani, don haka su ake ɗorawa laifi ya zamar musu babban abin damuwa a harkar kasuwancinsu."

Sai dai ya ce matsalar rage yawan kayayyakin ba daga wurinsu take ba, ta samo asali ne daga kamfanoni.

"Kamfanoni su ne suke rage yawan kayayyakin, wani lokacin ma har ingancinsu suke ragewa, kuma mu ma abin na shafar mu," in ji shi.

Amma kuma duk da hakan ya ce kamfanonin ba wai sun ƙara kuɗi ba ne, a maimakon rage inganci ko kuɗin kayan ne sai su rage yawan su.

''Kamfanoni ba su ƙara kuɗi ba gaskiya, amma sun rage yawan kayayyakin, yawanci idan ka ɗora kayan da aka rubuta nauyin giram goma a kan sikeli, sai ka taras nauyin bai wuce giram takwas ba,'' in ji malam Ibrahim.

Ƴan kasuwar sun kuma ƙara da cewa a fahimtarsu, kamfanonin ne suka samu ƙari kuɗi a irin kayan aikinsu su kuma da suka ga ba za su iya ƙara kuɗin ba suka gwammace su rage yawan kayan.

"Mu kuma a hannu guda idan muka sayo su a kan farashin da muka saba daga kamfanoni, to batun jigilarsu kawo su da dakonsu za a ga cewa kuɗin sufuri ya ƙaru matuƙa, kuɗin hayar shago ya ƙaru, abubuwa da dama sun hau.

"Kenan dole muma sai mun ƙara kuɗaɗe a kan farashin da muka sayo ɗin don mu fita, tun da ba a kasuwanci don a faɗi sai don riba," a cewar ɗaya daga cikin ƴan kasuwar da ya buƙaci a sakaya sunansa.

Wannan layi ne

Me masana ke cewa game da hakan?

Dakta Mohammed Shamsudden, wani masani kan harkokin tattalin arziki a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa sanannen abu ne cewa hauhawar farashin kayayyaki a kasar ya ta'azzara, inda a kusan kowane wata ake samun ƙaruwar farashin da ya tasar wa kashi 18% na farashin kayan masarufi.

Ya kuma ce don haka kamfanoni musamman wadanda ke sarrafa kayayyakin amfanin yau da kullum suna yi ne domin cin riba, don haka idan har suna son su ci riba dole sai sun yi yadda ba za su rasa masu sayen kayansu ba.

"A ganinsu wataƙila idan suka ƙara farashi to masu sayen kayan nasu za su daina saye saboda tsada."

"Don haka sai suka ɓullo da dabara, a maimakon ƙara farashin sai su rage wa kayan yawa ko nauyi ko wani fasali ko nagarta, kin ga a hakan an ƙara farashin kayan ne ta hanyar dabara", a cewarsa.

Short presentational grey line

'Hauhawar farashi ne a fakaice'

Dakta Mohammed Shamsuddeen ya kuma bayyana cewa tashin farashin kayayyaki na da sigogi daban-daban ta yadda ba kowa zai iya fahimtar me ake ciki ba.

"Shi hauhawar farashin kayayyaki ba wani abu ba ne, faduwar darajar kudi ne, misali idan ya zama kudi bai iya sayen adadin da a da zai iya saya ba shi ake kira hauhawar farashi, don haka shi ma wannan salo da kamfanonin suka ɓullo da shi nau'i ne na hauhawar farashi amma a fakaice,'' in ji masanin.

Ya ƙara da cewa babu shakka abubuwan da aka ragewa yawa ko nagarta a Najeriya suna da yawa, kuma mafiya yawa manya-manyan masana'antu da ba a yi tunani za su aikata hakan ba su ne suka yi.

Galibin irin wadannan kayyaki da aka ragewa yawa ko nagarta wadanda ke ƙunshe a cikin mazubai ne na kwali ko kuma leda.

Bayanan bidiyo, Tsadar rayuwa: Shin N30,000 za ta iya magance matsalolinku

Amma kuma akwai abubuwa ƙanana da ake sarrafawa a cikin gida kamar su rake da sauran abubuwan da ake auna nauyinsu ko kuma tsawon su.

Short presentational grey line

Ƙarin labarai masu alaƙa

Short presentational grey line

Daga ina matsalar ta fito?

Tushen matsalar dai kamar yadda Dakta Shamsuddeen ya bayyana daga kamfanonin ko kuma masana'antun take.

"Ba sa bin ƙa'idojin kasuwanci, misali za a rubuta nauyin kamar giram 50 a jikin kaya amma idan aka auna a sikeli za ka tarar bai kai nauyin haka ba."

Niara 500

Asalin hoton, Getty Images

Sai mai sharhin ya kuma ce duk da cewa akwai laifin masana'antu, ita ma gwamnati tana da nata laifin.

"Tun da su masana'antun an san suna yi ne don riba don haka idan babu wani wanda zai riƙa lura da abubuwan da ke faruwa don a magance, to lallai za su rika cin karensu babu babbaka, ta yadda za su rika samun riba in dai suna tunanin mai saye ba zai gane ba.

"Amma ita gwamnati tun da har muna da hukuma mai kula da nagartar kaya, ita ce ya kamata ta lura da cewar waɗannan abubuwa sun kai nagartar da suka kamata, kuma duk kamfanin da ya yi wata almundahana a hukunta shi,'' in ji masanin.

Masanin ya kuma zargi hukumomin gwamnati irin su hukumar kare muradan masu sayen kayayyaki ta ƙasa Consumer Protection Council da hukumar da ke tabbatar da ingancin kayayyacki SON, da rashin bin diddigin yadda kamfonin ke tafiyar da lamarinsu.

"Ba sa bibiyar abubuwan da ke faruwa ko kuma suna bibiya amma ba sa taɓuka komai,'' in ji Dakta Shamsudden.

Jihohin da kayan abinci suka fi tsada a Najeriya. A watan Fabrairun 2021. .

Masanin dai ya ce idan aka ci gaba da tafiya a hakan za a iya cewa za a sake shiga tsaka mai wuya, saboda idan aka hana kamfanonin rage yawa da kuma nagartar ko nauyin kayan dole ne su kara farashi.

"Saboda komai ya yi tsada a Najeriya, hatta makamashin wutar lantarki da man fetur da na diesel da ake amfani da shi a masana'antu, hatta ledoji da ake sarrafawa wajen zuba kayyakin sun yi tsada su ma,''in ji shi.

Ya kuma ce idan kuma ba a hana kamfanonin wannan almundahana ba, wataƙila idan wannan dabarar rage yawan kayan ta zama ruwan dare nan gaba duka nagartar kayayyakin gabaki daya a Najeriya za ta iya sauka, wanda kuma daga karshe dai talaka shi ne zai fi shan wahala.

''Akwai kuma yiwuwar waɗanda ke sayen kayayyakinmu daga ƙasashe maƙwabta su daina saboda faduwar nagartarsu,'' in ji masanin.

Short presentational grey line

Me hukumomi ke yi?

BBC ta tuntuɓi hukumar SON don jin ko me take yi kan wannan salo na kamfanonin?

Mai magana da yawun hukumar ya ce ba su taɓa samun ƙorafi daga wajen ƴan kasuwa ko wata ƙungiya ko tsirarun mutane kan wannan batu.

"Hukumarmu na aiki ne kan ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar mata, inda mu kuma za mu bincika, in dai mun gano wannan matsala to tabbas za mu tuntuɓi kamfanonin nan kuma za mu yi maganin abin.

"Don haka a yanzu dai ba mu samu ƙorafi ko ɗaya ba amma tabbas da zarar mun samu za mu ɗau mataki," a cewarsa.

Wannan layi ne