Ƙalubalen da ke gaban kwamitin da Buhari ya naɗa domin fitar da ƴan Najeriya miliyan 100 daga talauci

Asalin hoton, Getty Images
Masana kan harkokin da suka shafi ci gaba a duniya sun fara tofa albarkacin bakin su game da kwamiti na musamman da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada da aniyar rage talauci a tsakanin 'yan kasar.
A ranar Talata ne ya ayyana mataimakinsa Yemi Osinbajo a matsayin mutumin da zai jagoranci kwamitin mai kunshe da manyan jami'an gwamnati da ministoci.
Ya dauki matakin ne a yayin da Bankin Duniya ya ce hauhawar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya na kara talaucin da kuma tabarbarewar harkokin kasuwanci.
Bankin ya ce kimanin 'yan kasar miliyan bakwai ne suka fada cikin talauci a shekarar 2020 saboda tashin farashin kawai.
Kididdiga ta nuna cewa kusan kashi 75 bisa dari na al'ummar Najeriya ne suke fama da talauci iri daban-daban kamar fatara, da yunwa, da kuma irin da yau fari gobe baki.
Sai dai masana harkokin ci gaba sun dora alamar tambaya kan hanyoyin da ake bi wajen fitar da 'yan Najeriya daga talauci suna masu cewa dole ne kwamitin ya dauki matakai na zahiri wajen fuskantar kalubalen da ke gabansa.
A tattaunawarsu da BBC, Dakta Husaini Abdu, daraktan kungiyar Care International, wata kungiya mai yaki da talauci a duniya, ya ce duk wanda ya san yanayin da tattalin arzikin Najeriya yake ciki da kuma faman da ake yi da talauci, da yunwa da fatara, zai san cewa fitowa a yi yaki da talauci muhimmin aiki ne na gwamnatin kasar, da ta jihohi da kuma kananan hukumomi.
Ya kuma ce wannan kwamiti da Shugaba Buhari ya kafa ya zo a daidai lokacin da ake tsananin bukata, ko kuma ma za a iya cewa kusan an makara a wajen kafa shi idan aka yi la'akari da matsanin talaucin da 'yan kasar suke ciki.
Amma ya ce duk da haka matakin ya nuna cewa gwamnatin na da niyyar yaki da talauci da ya dabaibaye kasar.
"Saboda wannan gwamnatin ta kai shekara shida tana kan mulki, duk kuwa da cewa mun san ta fitar da kudade daban-daban na yaki da talauci, amma ba a kafa wani kwakkwaran kwamiti da aka dora wa aiki na yaki da talauci a Najeriya ba," in ji shi.

Kalubalen da ke gaban kwamitin
Kwamitin ya kunshi mambobi da suka hada da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, da wasu gwamnonin jihohin kasar, da wasu ministoci Najeriyar.
Dakta Hussaini Abdu ya ce akwai babban kalubale a gaban su saboda ya kamata a ce an hada da kwararru da kuma kungiyoyi masu zaman kansu a cikin kwamitin don samun nasarar gano hanya mafi sauki da za a bi wajen warware matsalolin talauci a kasar.
"Baya ga saka kungiyoyi masu zaman kansu ya kuma ce akwai bukatar saka 'yan kasuwa, da wakilan mata da matasa a cikin kwamitin.
"Idan ka dubi kasar nan babu wani yanki da yake fitowa karara yana yaki da talauci a Najeriya kamar kungiyoyi masu zaman kansu, don haka suna da matukar muhimmanci," a cewarsa.
Masanin ya kara da cewa: "Idan aka hada irin wadannan mutane a ciki, ta nan ne za a tabbatar da cewa gwamnati za ta yi aiki kamar yadda ya kamata saboda akwai wadanda suke da kwarewa a kan yadda ake yaki da talauci. Duk da cewa aikin gwamnati ne kamata ya yi a bambanta tsakanin mene ne aikin gwamnati da kuma a wane fanni ne ita gwamnatin ta kware."
Dakta Hussaini Abdu ya idan ba a hada hannu da kwararru ba kan warware matsalar talaucin da ta addabi 'yan Najeriba tarihi zai ci gaba da maimaita kansa na yadda aka saba nada irin wannan kwamiti amma kwallliya ta ki biyan kudin sabulu.
"Galibi irin wadannan kwamitoci babu abin da suke yi baya ga zaman tattaunawa a sha shayi a rubuta kasafin kudi a watse ba tare da cimma wani burin da ake bukata ba," in ji shi.
Muhimman abubuwan da suka kamata kwamitin ya yi la'akari da su
Yayin da yake yi wa BBC tsokaci game da kalubalen da ke gaban kwamtin yaki da talaucin na shugaba Buhari, Dakta Hussaini Abdu ya kuma zayyana muhimman abubuwan da yake gani ya kamata kwamitin ya fuskanta wajen cimma burin da ake bukata da fitar da 'yan Najeriyar daga kangin talauci kamar haka:
- Talaka da 'yayan talakawa(matasa kenan) su samu ayyukan yi.
- A samu a gina asibitoci ingantattu ta yadda idan talaka ya gamu da rashin lafiya zai samu kulawa ba tare da ya kashe makudan kudade wajen neman lafiya ba.
- Dan talaka ya samu ingantaccen ilimi
- A bunkasa ayyukan gona don samar da wadataccen abinci da samun kudaden shiga, kuma ya zamana ba sai mutanen karkara kadai ba za su yi aikin gona ba.
- Yanayin talaucin kasar nan ya fi shafar mata da matasa, don haka akwai bukatar zayyanawa karara abubuwan da za a yi wa mata ta yadda za su amafana.
- Wannan kwamiti ya yi kokari ya fadada shirinsa domin ya janyo kwararru da za su iya taimakawa da shawarwarai don ganin an tabbatar da cewa an cimma buri.
Shin Najeriya za ta iya kwaikwayon kasashen India da China?
A jawabin Shugaba Buharin wajen kaddamar da kwamitin ya bayar da misali da yadda aka yaki talauci a kasar India yana mai cewa idan har India za ta iya fitar da mutane miliyan 271 daga kangin talauci tsakanin shekarar 2006 zuwa 2016, tabbas Najeriya ma za ta iya cire mutane miliyan 100 daga talaucin a cikin shekaru 10.
Amma kuma Dakta Hussaini Abdu ya bayyana cewa a kasar nan akwai wadanda suke da wannan kwarewar da fahimtar da aka yi amfani da su aka yaki talauci a wasu kasashen, sai dai a a nan gizo yake sakar ba.
"Abin tambaya a nan shi ne ta yaya aka bi aka yi yaki da talaucin, kuma ta yaya kasashe kamar su India da China suka yi yaki da talauci? Za a iya amfana da kwarewarsu idan aka janyo irin wadannan kwararru a cikin kwamitin, ba lallai ba ne a kafa kwamiti a ce sai mutanen gwamnati," in ji masanin.












